Fararen hula na fama da sarkewar numfashi a Syria

Mata da kananan yara sun fi shan wahala a yakin Syria
Bayanan hoto,

Fararen hula na kwance a asibiti, bayan zargin gwamnati ta yi amfani da makami mai guba na sinadarin Chlorine

Jami'an lafiya a yankunan da 'yan tawaye suka yi wa kawanya a gabashin garin Ghouta na kasar Syria, sun ce daruruwan mutane na fama da matsalar toshewar numfashi sakamakon shakar iskar gas mai sinadarin Chlorine a hare-haren da dakarun gwamnati da na 'yan tawaye suka kai wa juna.

A wata sanarwa da ministan lafiyar kungiyar 'yan a ware ya fitar, ya ce mutanen da lamarin ya rutsa da su da suka hada da fararen hula da direbobin motocin daukar marasa lafiya sun kwanta a asibiti sakamakon shakar iskar da suka yi bayan fashewar wani abu.

Wani mazaunin garin Ghouta ya shaidawa BBC cewa dakyar wani yaro ya rayu sakamakon numfashinsa da ya sarke, ana dai zargin gwamnatin Syria da amfani da makamai masu guba kokarin fatattakar 'yan tawayen daga maboyarsu.

A ranar asabar ne aka kada kuri'ar amincewa da dakatar da bude wutar tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta a birnin New York na Amurka.

Amma duk da hakan an ci gaba da kai hare-hare nan da can. Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kananan yara sun fi shan wahala a yakin da ake yi a Syria.

Sama da shekara 4 kenan ana yakin na Syria, tun bayan kadawar guguwar sauyi a yankin gabas ta tsakiya. A bangare guda kuma 'yan tawaye sun sha damarar kawo karshen mulkin shugaba Basharul Assada na Syria amma har yanzu hakarsu ba ta cimma ruwa ba.