Ana ci gaba da alhinin rasuwar jaruma Sridevi

Sridevi ta fito a fina-finai kusan 300 na Hindi da Telugu da kuma Tamil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sridevi ta fito a fina-finai kusan 300 na Hindi da Telugu da kuma Tamil

Dubban masoya da jarumai da ma masu ruwa da tsaki a bangaren fina-finan Bollywood ne ke kwarara gidan marigayiya Sridevi, wadda ta rasu a daren ranar Asabar a Dubai.

Jarumar, ta rasu ne sakamakon bugun zuciya tana da kimanin shekara 54 a duniya a lokacin da ta je Dubai domin halartar bikin daya daga cikin 'yan uwansu.

Sridevi, ta je bikin ne tare da mijinta Boney Kapoor da kuma 'yarta Khushi.

Marigayiyar ta fito a cikin fina-finai kusan 300, da suka hadar da na Hindi da Tamil da kuma na Telugu a cikin shekara 50 da ta shafe tana fim.

Ta fara fim ne tun tana karama, wato shekara hudu da haihuwa.

Ana dai ganin jarumar ta na daga cikin jarumai mata na India da suka samu nasara a sana'arsu ta fim, saboda irin nasarorin da ta samu.

Labarin rasuwarta ya tayar da hankulan mutane da dama, ba ma a kasar India kadai ba, har ma da sauran kasashen da ke kallon fina-finan India kamar Najeriya.

Asalin hoton, CITY TIMES INDIA

Bayanan hoto,

Mutane sun hallara a kofar gidan jaruma Sridevi domin jiran isowar gawarta daga Dubai

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A yanzu haka, mutane sun yi dafifi a kofar gidan jarumar da ke Mumbai, domin jiran isowar gawarta, wadda majiyoyi suka ce za a kawo ta a ranar Litinin daga Dubai, bayan kammala gwaje-gwajen da likitoci suka yi.

Jaruman Bollywood da dama sun hallara a gidan kanin mijin Sridevi, wato Anil Kapoor, inda suke lallashin babbar 'yarta, Jhanvi Kapoor, wadda suka bari a gida.

Jarumai kamar Rekha da Karan Johar da Arjun Kapor wanda yayane ga 'yar Sridevin da suka hada uba da Sonam Kapoor da Rani Mukherje da dai sauransu duk suna tare da 'yar gidan marigayiyar.

Kazalika sauran jarumai kamar Priyanka Chopra da Shahruk Khan da Aamir Khan da Salman Khan da Kajol da Akshay Kumar da Madhuri Dixit da Rishi Kapoor, daya daga cikin jarumai mazan da ta yi fina-finai da dama dashi da Jeetandra wanda ta fara fim din Hindi tare da shi da Amita Bachchan da Hema Malini da Kamal Hassan da Anupam Kher da Farhan Akhtar da Vivek Oberoi da dai sauransu duk sun wallafa alhininsu game da rasuwar jarumar a shafukan su na twitter.

A ranar Litinin ne dai ake sa ran isowar gawar jarumar gida India domin yi mata jana'iza.

Sridevi ta rasu ta bar mijinta da 'ya'ya biyu mata wato Jhanvi da Khushi Kapoor.