Jami'an tsaron Nigeria sun bazama neman 'yan matan Dapchi 110

Sandals are strewn in the yard of the Government Girls Science and Technical College in Dapchi, Nigeria. Photo: 22 February 2018 Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption An bar takalma a warwatse bayan sace 'yan matan na Dapchi

Gwamnatin Najeriya ta tura karin dakarun tsaro da jirage domin nemo 'yan mata 110 da aka yi amannar cewa kungiyar Boko Haram ce ta sace su a makon jiya.

Mayakan Boko Haram sun shiga garin Dapchi da ke jihar Yobe ranar 19 ga watan Fabrairu, inda suka ya da zango a makarantar 'yan matan, suka yi awon gaba da su.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce satar yaran wani "babban bala'i ne" sannan ya nemi afuwar iyayen matan kan abin da ya faru.

Wannan lamari ya tuna wa duniya sacewar da 'yan Boko Haram suka yi wa 'yan matan makarantar sakandaren Chibok a shekarar 2014.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata uwa da aaka sace wa 'ya a Dapchi

Iyayen yaran sun nuna matukar rashin jin dadinsu a daidai lokacin da rahotanni ke cewa sojoji sun janye daga wuraren binciken ababen hawa da ke Dapchi wata guda kafin aukuwar lamarin.

Sojojin sun amince cewa sun janye dakarunsu daga wuraren gabanin kai harin.

An kai hari a Dapchi, wanda ke da nisan kilomita 275k daga Chibok, ranar Litinin din makon jiya, lamarin da ya sa dalibai da malaman Makarantar Koyon Kimiyya da Fahasa ta mata suka ranta a na kare zuwa cikin dazukan da ke kusa

Mazauna yankin sun ce jami'an tsaron kasar, wadanda jiragen yaki ke rufa wa baya, sun dakile harin.

Da farko dai gwamnatin jihar ta ce babu wanda aka sace, tana mai cewa daliban sun buya ne domin gudun kada maharan su kama su.

Amma daga bisani sun amince cewa an sace mata 110 bayan harin.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyayen matan da aka sace a Dapchi na duba jerin sunayen 'ya'yansu

Labarai masu alaka