Bidiyon yarinyar da ke kukan jini

Bidiyon yarinyar da ke kukan jini

A duk lokacin da Nikki Christou mai shkera 13 ke kuka sai jini ya dinga fitowa daga idonta maimakon hawaye.

Nikki na fama ne da wata cuta da ke da alaka da jijiyoyin da jini ke bi wacce ake kira arteriovenous malformation, AVM, al'amarin da ke sa take kukan jini wanda hakan ke barazana ga rayuwarta.

A yanzu masana kimiyya sun gano abun da ke jawo wannan cutar da ba a saba gani ba, kuma sun yi amanna magunguna sankara za su iya taimakawa Nikki, don haka a yanzu ana amfani da ita wajen gwajin da masana kimiyya ke yi a Cibiyar Lafiyar Yara da ke Jami'ar Landan da kuma Asibitin Ormond Street.