Sojoji sun fice Dapchi ba da saninmu ba- 'Yan sanda

Makarnatar Dapchi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An sace 'yan matan makarantar Dapchi bayan sojoji sun fice

Rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta musanta ikirarin da rundunar sojin Najeriya ta yi cewa ta hannunta ragamar tafiyar da tsaro ga 'yan sanda kafin ta janye jami'anta.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan 'yan sandan jihar Yobe Sumonu A Abdulmaliki ya ce sanarwar da rundunr lafiya dole ta fitar game da mika ragamar tafiyar da tsaron Dapchi ga 'yan sandan ba gaskiya ba ne.

Sanarwar ta ce babu wani lokacin da Sojojin suka sanar da 'yan sanda, ko tuntubar su kafin su fice a hukumance daga garin Dapchi balle har su hannunta ma su ragamar tafiyar da tsaron garin.

Sanarwar kuma ta bukaci jama'ar Yobe su yi watsi da ikirarin na sojojin, domin ba gaskiya ba ne.

Sanarwar 'yan sandan na zuwa ne bayan, rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwa da ke dauke da bayani a kan dalilin da ya sa sojoji suka janye kafin harin da aka sace 'yan matan makarantar Dapchi sama da 100.

Rundunar Lafiya dole ta ce jami'anta sun janye ne kasancewar kura ta lafa a yankin na Dapchi, kuma yanzu aikin 'yan sanda ne su ci gaba da samar da tsaro a yankin.

Tun da farko dai gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam yi fito ya dora laifin a kan gazawar sojoji na rashin kula da tsaron makarantar da har 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka samu kwarin guiwar shiga su sace daliban.

Labarai masu alaka