Burkina Faso: Za a fara shari'ar wadanda suka kitsa juyin mulki

An girke daruruwan jami'an tsaro a wajen harabar kotun da za a yi shari'ar mutanen da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An girke daruruwan jami'an tsaro a wajen harabar kotun da za a yi shari'ar mutanen da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso

A ranar Talata ne za a fara shari'ar mutanen da ake zargi da yunkurin juyin mulki a shekarar 2015 a kasar Burkina Faso.

Fiye da mutum 80 ne za su bayyana gaban kotu a shari'ar da aka bayyana a matsayin zakaran gwajin dafi a tsarin shari'ar kasar.

Daruruwan jami'an tsaro aka girke a harabar kotun wadda za a fara shari'ar wadannan mutane.

Daga cikin mutum 80 din da zasu bayyana gaban kotun har da wasu manyan janar biyu fitattu wato Gilbert Diendere da kuma Djibril Bassole, wadanda na hannun daman tsohon shugaban kasar Blaise Compaore ne.

A waccan gwamnatin da ta shude, Gilbert Diendere, shi ne shugaban masu tsaron fadar shugaban kasar.

Ana kuma zargin sa shi da sojojin da ke karkashinsa da yunkurin hambarar da gwamnatin rikon ta Burkina Faso, shekara guda bayan tsohon shugaban kasar ya bar kasar.

Yayin da Janar Bassole, da sauran mutanen da za su bayyana gaban kotun kuma ake tuhumarsu da cin amanar kasa da yin zagon kasa ga harkar tsaron kasar da kuma kisa.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar na kallon wannan shari'a a matsayin zakaran gwajin dafi dangane da sahihancin tsarin shari'ar kasar.

A watan Satumbar shekarar 2015 ne, wasu daga cikin dakarun da ke tsaron fadar tsohon shugaba kasar suka kama wasu jami'an gwamnatin rikon kwarya.

To amma yunkurinsu na juyin mulkin da suka so yi, bai samu nasara ba saboda zanga-zangar da aka rinka yi a kan tituna da ta samu goyon bayan sojojin kasar.

Akalla mutum 14 sun rasa ransu, yayin da wasu fiye da 200 kuma suka samu raunuka a yayin zanga-zangar.

Labarai masu alaka