An mika gawar Sridevi Kapoor ga 'yan uwanta

Bayanan bidiyo,

Sridevi ta shahara sosai a Bollywood

'Yan sandan birnin Dubai sun kammala binciken da suka yi a kan gawar jarumar Bollywood Sridevi Kapoor sannan suka mika ta a hannun iyalinta.

Jarumar, mai shekara 54, ta mutu ne ranar Asabar "sakamakon nitsewar da ta yi a cikin ruwa", in ji 'yan sandan. An gano gawarta a wurin wankan da ke otal din da ta sauka.

Tunda farko an ba da rahoton cewa bugun zuciya ne ya kashe shi a lokacin da suka je bikin 'yan uwanta a Dubai.

Yanzu za a kona gawarta kafin a kai ta India inda za a yi mata jana'iza.

Tuni dandazon jama'a ya taru a kofar gidan Sridevi da ke Mumbai domin yi mata girmamawar karshe kafin a yi mata jana'iza.

Ta soma fitowa a fina-finan Bollywood tana da shekara hudu.

Sridevi ta soma fitowa a manyan fina-finai a 1978, inda daga nan ne ta zama daya daga cikin manyan jaruman India.