An soma bikin binne Sridevi Kapoor

Bayanan bidiyo,

Sridevi ta yi suna sosai a masana'antar Bollywood

Dubban masoyan tauraruwar Bollywood sun taru a birnin Mumbai da ke Indiya don su yi jana'izar Sridevi Kapoor, wadda ta mutu a Dubai ranar Asabar.

Masoyan nata sun yi layi a wani wuri da ake kira Celebrations Sports Club kafin jana'izar ranar Laraba, kuma suna rike da furanni da hotuna.

A daren Talata ne aka kai gawarta Indiya.

'Yan sanda sun ce 'yar wasan kwaikwayon, mai shekara 54, ta rasu ne sakamakon nitsewa a wurin wanka bayan ta fita daga hayyacinta.

An gano gawarta a cikin kwamin wanka a otal din da ta sauka a Dubai.

Tunda farko an ba da rahoton cewa bugun zuciya ne ya kashe shi a lokacin da suka je bikin 'yan uwanta a Dubai.

Ta soma fitowa a fina-finan Bollywood tana da shekara hudu kuma ta yi fina-finai sama da 300

Bayanan hoto,

Mutane dayawa sun taru don su yi jana'izar ta

'Yan wasan kwaikwayo Aishwarya Rai da Kajol na cikin mutanen da suka halarci makokinta a wani wurin rawa da ke Andheri West a Mumbai, inda ake kira gidan Bollywood.

Wata masoyiyar jarumar mai suna Nandini Rao ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "abin mamaki ne cewa Sridevi ta rasu, muna so mu yi mata kallon karshe a yau."

An girke 'yan sanda da dama a gidan tauraruwar, da kuma kan hanya da wajen Vile Parle Seva inda za a kona gawarta.

Ana sa rai dubban masoyanta za su halarci jana'izar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutuwar Sridevi ta girgiza mutanen Indiya

Asalin hoton, AFP