Jirgin sama ya jawo cunkoso a titin motoci a Afirka Ta Kudu

Afirka Ta Kudu

Asalin hoton, Nasidi Yahaya

Al'ummar birnin Johannesburg a kasar Afrika Ta Kudu sun tashi sun iske tsananin cunkoson ababen hawa sakamakon jan wani jirgin sama da ake yi a kan titin.

An ce mazaunan garin sun saba da samun cunkoson ababen hawa, amma ba su taba ganin inda jirgin sama ya janyo hakan ba.

An yi ta jan jirgin saman mai tsawon mita 40 daga wani wuri mai suna Jet Park daga gabas, zuwa Fourways Mall a arewa, inda zai zama wani ɓangare na sabon filin wasa da ake kira Kidzania.

Abun ya bai wa yara da dama sha'awa ganin jirgin sama a titin motoci, amma ya zama abun takaici ga masu tafiya, wadanda suke korafin me ya sa aka zabi ranar Talata don jan jirgin.

Asalin hoton, Nasidi Yahaya

Asalin hoton, Nasidi Yahaya