Yadda mata ke yi wa jarirai bilicin tun suna ciki a Ghana

Ghana

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mata ma su juna biyu na shan kwayar Glutathione don yi wa jarirai bilicin

An gargadi mata a Ghana game da shan wasu kwayoyin bilicin a yayin da suke dauke da juna biyu da nufin sauya fatar jariran da ke cikinsu.

Masana kiwon lafiya sun ce kwayoyin da matan ke sha za su iya haifar da illa a wajen haihuwa da yin lahani ga koda da kuma lalata gabban jikinsu.

Hukumar FDA da ke kula da ingancin abinci da magani ta ce shan kwayar Glutathione ga mata masu juna biyu abu ne mai matukar hatsari.

Hukumar ta gargadi jama'a cewa babu wani magani da ta amince da shi domin bilicin jaririan da ba a haifa ba.

Tabi'ar na ci gaba da girma a Ghana, a cewar hukumar, kuma mutane na shigo da kwayoyin ne da dama ta hanyar boye su cikin jikar kayansu a tasoshin jiragen sama.

Ko da yake babu wasu bayanai da aka tattara game da girman matsalar, amma hukumar ta ce binciken da ta gudanar ya taimaka wajen bayyana halin da matan ke ciki.

Yanzu haka jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike domin cafke kamfanoni da mutanen da ke hakarar shigo da kwayoyin.

A watan da ya gabata ne Hukumar shige da fice ta soke cancantar matan da fatar jikinsu ta nuna suna bilicin daga cikin sabbin ma'aikatan da za ta dauka aiki.

Hukumar ta dauki matakin ne saboda dalilai na tabbatar da lafiyar jami'anta.