Dapchi: Gwamnatin Nigeria za ta kaddamar da kwamitin bincike

Kwamitin zai duba yadda jami'an tsaro ke ayyukansu a Dapchi da kuma makarantar kafin sace daliban Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Kwamitin zai duba yadda jami'an tsaro ke ayyukansu a Dapchi da kuma makarantar kafin sace daliban

Gwamnatin Nigeria za ta kaddamar da kwamiti domin gudanar da bincike kan yadda aka sace 'yan matan sakandaren Dapchi 110 da ke jihar Yobe a arewacin kasar makon da ya gabata.

Kwamitin mai mabobin 12 ya kunshi sojojin kasa da na ruwa da na sama da kuma 'yan sanda da hukumar tsaro ta SSS da ta Civil defence.

Daga cikin ayyukan kwamitin da za'a kaddamar ranar laraba sun kunshi binciken dalilan da ke tattare da sace wadanan 'yan mata.

Haka kuma kwamitin zai duba yadda jami'an tsaro ke gudanar da ayyukansu a Dapchi da kuma makarantar kafin sace daliban.

Har ila yau, ana saran kwamitin zai gabatar da shawarwari da za'ayi amfani da su wajen gano inda aka kai 'yan matan da kuma yadda za'a ceto su.

Rahotanni sun ce an bai wa kwamitin zuwa ranar 15 ga watan Maris na 2018 ya gabatar da bayanan da ya tattara.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da sojoji da 'yan sanda ke musayar yawu kan rundunar da ke da alhakin ba garin na Dapchi tsaro lokacin da 'yan bindiga suka kai hari.

Labarai masu alaka