An rufe coci 714 saboda karya doka

Majami'un ba su sabunta lasisinsu ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Majami'un ba su sabunta lasisinsu ba

Hukumomi a Rwanda sun rufe coci sama da 700 a Kigali, babban birnin kasar saboda sun karya dokokin tsaro da kiwon lafiya, in ji jaridar The New Times mai zaman kanta.

Sun ce an soma rufe majami'un ne a makon jiya kuma zuwa yanzu an rufe coci 714 da masallaci daya.

Wani jami'i, Justus Kangwagye, ya shaida wa jaridar cewa wuraren ibadar sun keta dokokin tsaro.

"Ya kamata a rika yin ibada a cikin yanayi mai aminci da tsaro. Bai kamata mutum ya karya doka ba a yayin da yake son gudanar da ibada. An ba su umarni su daina gina wuraren ibadar har sai sun cika sharudan tsaro," in ji shi.

Ya kara da cewa wasu majami'un ba su sabunta lasisinsu ba don haka hukuma ba za ta bari su ci gaba da gudanar da ibada a wuraren ba.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin cocin suna yin ibadarsu ne a cikin tantuna kuma ba su da wuraren ajiye ababen hawa, inda masu ibada ke ajiye ababen hawarsu a kan titi abin da ke jawo cunkuso a hanya.

Rahotannin sun kara da cewa mazauna birnin Kigali sun bayyana ra'ayoyi mabambanta kan wannan mataki. Wasu sun goyi bayan matakin yayin da wasu suka ce bai dace ba.

Shugaban kungiyar majami'u na lardin Nyarugenge, Bishop Innocent Nzeyimana, ya roki gwamnati ta dakatar da matakin da ta dauka zuwa lokacin da cocin za su gyara matsalar.