An zargi Koriya Ta Arewa da bai wa Syria makamai masu guba

A Syrian man wears an oxygen mask at a make-shift hospital following a reported gas attack on the rebel-held besieged town of Douma in the eastern Ghouta region on the outskirts of the capital Damascus on January 22, 2018.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana samun rahotannin cewa ana kai harin makamai masu guba gabashin yankin Ghouta

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya bayyana, ya nuna cewa Koriya ta Arewa na aikawa Syria wasu abubuwa da a ke amfani wajen sarrafa makaman nukiliya ta jiragen ruwa.

Rahoton da masana a MDD su ka rubuta, wanda kuma jaridu da dama su ka gani, ya ce abubuwan da a ke aikawa sun hada da tayil-tayil da wanda asid ba ya iya bata su da na'urorin auna yanayi wato thermometer.

Haka kuma, rahoton ya ce an sha ganin wasu ma'aikatan Koriya Ta Arewa su na aiki a wuraren sarrafa makamai a cikin Syria.

Gwamnatin Syria dai ta yadda a rushe ma'adanar kemical din ta bayan wani harin gas din Sarin da ya kashe daruruwan mutane a Ghout a shekarar 2013, amma ko bayan nan an tuhume ta da kai hare-haren kemikal.

Rahoton ya ce a baya an shigar da irin wadannan kaya sau 40 tsakanin shekarar 2012 zuwa ta 2017.

Wannan zargi dai ya biyo bayan sabon rahoton da aka samu cewa dakarun Syria su na amfani da makamai masu guba, amma gwamnatin kasar ta yi watsi da wannan zargi.

Sai dai an yi ta jin karar hare-haren sama a yankin Gabashin ghouta da ke wajen birnin Damascus bayan da aka shiga kwana biyu na dakatar da fadan da ake yi don a samu damar shigar da kayan agaji.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Masu fafutuka dai suna zargin hare-haren kasa da na sama da gwamnati ke kai wa ya hana a shigar da kayan agaji ga fararen hula, yayin da Rasha kuma ke zargin 'yan tawaye.

Wadannan zarge-zarge ake yi wa Koriya Ta Arewa?

Kasashen duniya dai sun kakabawa Koriya Ta Arewa takunkumai kan shirin makami mai linzaminta.

Amma wani rahoton sirri da wata tawagar kwararru na Amurka ta hada, wanda ya yi duba kan yadda Koriya Ta Arewa ke yn biyayya ga dokokin MDD, ya gano cewa ta karya dokoki wajen aikewa da kayayyakin Syria.

Rahoton wanda BBC ta gani ya ce kayayyakin sun hada da tayil-tayil da wanda asid ba ya iya bata su da na'urorin auna yanayi wato thermometer.

An yi zargin cewa wata cibiyar kimiyya ta gwamnatin Syria SSRC ce ta biya Koriya Ta Arewa kudaden kayan ta hannun wasu kamfanoni.

Gwamnatin Syria na tallafawa cibiyar SSRC a matsayin cibiyar bincike ta farar hula, amma Amurka ta zargi cibiyar da mayar da hankali kan hada makamai masu guba.

Bayanan bidiyo,

Kalli rawar sojojin Korea ta Arewa