'Ina daukar kaina hoto sau 200 duk rana'

Junaid Ahmed Hakkin mallakar hoto Junaid Ahmed/Getty Images

Junaid Ahmed yana da mabiya 50,000 a shafin sada zumunta na Instagram kuma ya ce yana jin dadin daukar hoton kansa sosai.

Matashin dan shekara 22 yana daukar a kalla hotuna 200 na kansa a rana.

Yana mayar da hankali wajen zabar lokacin da zai sanya hoto a kafofin sada zumunta saboda ya samu mutane da yawa su yaba hoton, kuma idan mutane kasa da 600 su ka yaba hoton, yana cirewa.

Junaid ya ce: "Idan na saka hoto, to a mintuna biyu na farko ina samun kamar mutane 100 da za su yaba kuma abun yanafaranta min rai sosai.

Wani binciken da aka yi baya-bayan nan a Jami'ar Nottingham Trent ya nuna cewa masu daukar hoton kansu na fama da wani ciwo ne mai alaka da tabin hankali da ake kira Selfitis.

Junaida ya ce yawan son daukar hoton kansa da ya ke yana jawo masa rashin jituwa tsakaninsa da masu kaunarsa.

Junaid ya ce a yanzu irin maganganun kushe da ake yi kan hotunansa ba sa damun sa kamar da - amma ya fallasa cewa an masa tiyatar kwaskwarima a fuska saboda matsin lambar da ya ke fuskanta daga kafofin sada zumunta.

Ya ce an mayar masa da hakoransa farare an gyara masa haba da kumatu da mukamiki da labba da kasan ido da kai da sanya masa gashin ido da kuma rage masa kiba.

Hakkin mallakar hoto Junaid Ahmed
Image caption Junaid mayen daukan hoton kan sa ne

Junaid wanda dan birnin Essex ya ce ya fahimci yadda mutum zai iya haduwa da adawa a kafofin sada zumunta, amma bai damu ba sosai.

Ya kuma ce abubuwan da mu ke gani a kafofin sada zumunta ba gaskiya ba ne.

Kafofin sada zumunta suna da dadin amfani, amma kada ku bari ya shafi rayuwarku ta wajen son zama abun da ku ka ga wasu sun zama."