Nigeria za ta yi karar Jami'ar Alabama ta Amurka

Alabama State University Hakkin mallakar hoto Alabama State University

Gwamnatin Najeriya za ta kai karar wata Jami'a a Amurka saboda ana zargin su da cinye kudin makarantar dalibai, da kudin masauki, littatafai, da kuma abincinsu.

Gwamnatin da hadin gwiwar wadansu daliban Najeriya da dama sun yi karar Jami'ar Jihar Alabama tun a shekarar 2016.

Kuma ana zargin jami'ar wadda take daukar dalibai bakaken fata, da amsar kudin masauki wanda ba su yi amfani da su ba, da cajansu kudin darasin da ba su dauka ba.

Jami'ar ta musanta cewa ta aikata ba daidai ba, kuma sun shaida wa kafofin yada labarai cewa, ba su saba kowace irin ka'ida da gwamnatin Najeriya ta gindaya musu ba a yarjejeniyar.

Ta bayyana cewa suna bin gwamnatin Najeriya $202,000 bayan da aka biya komai da komai, amma sun ce kuma an biya kudin.

Amma Anthony Ifediba wadda take wakiltar daliban ta ce jami'ar ta rike dala 800,00.

Ya shaida wa kamfanin Montgomery Advertiser cewa gwamnatin Najeriya ta biya jihar Alabama kimanin dala miliyan biyar, don biyan kudin makarantar dalibai da kudin kashewarsu.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka