Bakambu ne yanzu dan wasa mafi tsada a Afirka

Cedric Bakambu

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Jamhuriyyar dimukuradiyar Congo Cedric ya koma taka leda a kulub din Beijing Guoan na China.

Rahotanni sun ce kulub din Beijing Guoan FC, ya saye dan wasan a kan jimillar kudi da suka kai dala miliyan 90.

Yanzu Bakambu ya kasance dan wasa mafi tsada a Afrika inda ya sha gaban Pierre-Emerick Aubameyang dan wasan Gabon da Arsenal ta karbo daga Borussia Dortmund akan kudi dala miliyan 77.

Bakambu ya kulla yarjejeniyar shekaru 4 ne da kulub din na Beijing.

Tun a watan Janairu ne Bakaumbu ya fara atisaye tare da tawagar kulub din a wasannin share fagen kaka a Portugal.

Bakambu ya ci kwallaye 9 a La liga a bana kafin ya bar Villarreal a watan Janairu.

Shi ne dan wasan Afirka na farko da aka taba karramawa a matsayin gwarzon dan wasan La liga na wata.