Iran ta kama mata 35 don sun je filin kwallo

Magoyabayan tawagar 'yan kwallon kasar Iran a wani wasa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Maza kawai doka ta halarta wa zuwa filin kwallo a kasar Iran

Kasar Iran ta tsare mata 35 don sun je filin wasan kwallon kafa.

Matan suna kokarin kallon wani wasa ne tsakanin wadansu kungiyoyi da ke birnin Tehran wato tsakanin Esteqlal da Persepolis.

Iran ta ce an rike su ne na dan lokaci amma za ta sake su bayan wasan.

Shugaban hukumar kwallon kafa Fifa, Gianni Infantino, ya halatta filin wasan, tare da ministan wasannin Iran Masoud Soltanifar.

A cewar kamfanin dillancin labarai na ISNA, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje na kasar Seyyed Salman Samani ya ce ba a kama magoya bayan 'yan wasan kwallon kafa ba - amma 'yan sanda sun kai su wani wuri.

Wadansu rohatanni sun ce an rike mata biyu daga cikinsu.

Dokokin Iran sun hana mata zuwa kallon wasannin kwallon kafa tun bayan juyin juya halin Musulunci a Iran a shekarar 1979.