Dapchi: 'Bala'in da muka gani yayin da BH suka zo makarantarmu'

Dapchi

Satar dalibai 110 a makarantar sakandaren kimiya da fasaha ta 'yan mata da ke garin Dapchi a jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya, ta haifar da yanayi iri-iri ga rayuwar jama'ar garin da ma na wajen garin.

Kowa da irin labarin da yake bayarwa game da yadda abin ya shafe shi. Wata daliba, Fatima Awwal, na daga cikin wadanda suka tsira a harin. To amma tserewa da ta yi daga maharan ba ta raba ta da takaici da kuncin rayuwa ba.

Na rasa kawayena biyar

Ta shaida mani cewa cikin dalibai fiye da 100 da ake zargin 'yan Boko Haram suka sace akwai kawayenta biyar wadanda ta shaku da su kwarai da gaske. Akwai kuma wasu 'yan matan da dama da ta sani.

Fatima ta shaida mani cewa a lokacin da aka kai harin sai ''duk makarantar ta rikice…ana ta guje-guje "kuma muna jin karar harbe-harben bindigogi da ganin harsasai a sama kamar wuta na yawo''.

Lamarin ya faru ne yayin da daliban ke shirin cin abinci wasu kuma na shirin sallar Magariba. Fatima Awwal ta ce daya daga cikin kawayen nata, mai suna Zarah Tijjani, ta wanke masu tufafi ita kuma tana shirin kafin su yi barci za ta goge masu tufafin sai kwatsam suka fara jin karar harbe-harbe.

A cewarta, sun yi yunkurin fita ta babbar kofar makarantar amma sai suka tarar kofar na kulle abin da ya tilasta masu kokarin tsallaka katanga.

Fatima da wasu daliban da dama sun tsere ta hanyar tsallake katanga da kuma gudu na tsawon kilomitoci.

Dalibar ta bayyana mani cewa a lokacin da maharan suka iso sun kasu kashi-kashi ne: Gungu daya suka tsaya daga ta kusurwar da dakunan kwanan dalibai suke suna ta harbe-harbe, gungun na biyu kuma suka tsaya da motoci a gaban makarantar su ma suna harbi.

Ta ce maharan sun ma yi ta kiransu cewa su zo shiga motocin domin su cece su, abin da ya sa wasu daliban suka yi tsammanin sojoji ne ba 'yan bindiga ba.

Dalibar ta ce a ranar ita da wasu dalibai da suka tisra sun kasa cin abinci.

Na bai wa dalibai kusan 200 mafaka

Gidan Malam Tijjani Kalli dai gida ne na laka a garin na Dapchi. Ko da ya ke gidan ba shi da girma, to amma a lokacin da aka kai harin sace daliban sai girman gidan ya karu.

Ya shaida mani cewa 'yarsa mai suna Zarah na daya daga cikin dalibai a makarantar ta 'yan mata. Ya yi yunkurin ceto 'yar tasa amma rugugin bindigogi da wulgawar harsasai suka tilasta masa fasa yunkurin nasa.

"Da na ji karar harbe-harben bindiga a makarantar sai na ruga da gudu domin in je in dauko 'yata, amma ko da na isa kusa da katangar makarantar sai na ga bindiga da harsashi kusa da ni, don haka na kwanta a kasa, na kuma lallabo na dawo gida.''

Lokacin da na dawo gida sai na tarar da wasu daliban kusan 200 a cikin gidana suna samun mafaka. Ya yi ta bincikawa bai ga 'yar tasa ba, har ya fita zuwa wasu wurare a cikin daren domin nemanta, amma bai ganta ba.

Da gari ya waye sai ya fahimci cewa tana cikin wadanda 'yan bindiga suka sace. Wani abin damuwa a cewar Tijjani Kalli shi ne dukkan 'yan makarantar da lamarin ya shafa 'ya'yan talakawa ne , wasu ma marayu ne- ba uwa, ba uba.

"Babu 'ya'yan wani jami'in gwamnati a makarantar. Duka 'ya'yan talakawa ne irina.''

Shi da matarsa wato mahaifiyar yarinyar, sun nuna mani wasu daga cikin litattafan 'yar tasu mai suna Zarah kuma ga alama daliba ce mai kwazo domin na ga daya daga cikin jarrabawar da aka yi masu ta amsa duka tambayoyin daidai.

Mahaifiyarta mai suna Habiba, ta gaya mani cewa yarinya ce mai hankali da ilmin boko da na addinin Islama.

''Fatanmu shi ne idan suna raye Allah ya dawo da su, idan kuma sun mutu, Allah Ya ji kansu ya ba su makwanci mai kyau.'' In ji Habiba.

To amma ta roki hukumomin Najeriya da su kokarta domin ceto yaran daga hannun wadanda suka sace su.

Ita ma yayar Zarah mai suna Falmata, ta nuna rashin jin dadinta kwarai inda ta fashe da kuka a lokacin da na nake zantawa da ita kan abin da ya faru. Ta ce ''sun sace mana kanne! Yara ne kanana, shin me za su yi da su? Sun bar mu cikin bakin ciki.''

Gara mutuwa da sace 'yata

Hafsat Juluri mahaifiya ce da 'ya'yanta uku ke karatu a kwalejin 'yan matan ta garin Dapchi. A ranar da aka kai harin, biyu ne daga cikinsu ke makarantar domin dayar an maido ta gida kwana daya gabanin harin saboda lalurar rashin lafiya.

Image caption Daliban na daf da cin abincin dare lokacin da maharan suka je makarantar

Cikin yaranta biyu da ke makarantar a lokacin da aka kai harin, guda ta tsira yayin da gudar kuma ke cikin 'yan makaranta da 'yan bindiga suka sace.

Lokacin da na ziyarcin gidansu a garin na Dapchi, na tarar da yarinyar da ta tsirar mai shekaru 18 tare da mahifiyarta Malama Hafsatu Juliri suna jimanin wacce aka sacen.

Malama Juluri ta shaida mani cewa sace 'yar tata ba karamin tashin hankali ya jefa su ciki ba.

''Da irin wannan yanayi gara a ce mutum ya mutu ka ga gawarsa. Amma baka ga mutum ba, kuma ba ka ga gawarsa ba,'' a cewarta.

Ita ma dai sunan yarinyar da ta tsirar Hafsat, wato sunansu daya da mahaifiyarta. Ta shaida mani cewa sun rabu da kanwarta Hauwa ne a lokacin da suke gudun neman tsira.

Ta ce ''daya daga cikin mutanen (maharan) yana bi na yana cewa in kwanta, in fi ruf-da-ciki ko kuwa ya harbe ni. A lokacin ban ji tsoron bindigarsa ba, sai na ci gaba da gudu har na tsira.''

Malama Hafsat Juluri ta roki gwamnati da ta kara himma domin ceto 'yaran nasu.

''Tun bayan faruwar abin, ba mu samu wani bayani daga gwamnati ba. Ba wanda ya damu da halin da muke ciki in ban da mutane 'yan jarida irinku. Fatanmu shi ne mu samu yaranmu su dawo.

"Muna rokon Shugaba Muhammadu Buhari da sauran manyan masu fada a ji, da su yi kokari su ceto mana yaranmu.'' Mahaifiyar cikin murya mai sosai rai, ta numa damuwa kan halin da 'yan matan ke ciki.

''Allah Ya kare mana su a duk inda suke. Allah Ya tsare mana mutuncinsu. Idan suna raye Allah Ya dawo mana da su. Muna kuma rokon sauran jama'a su taya mu da addu'a."

Ba na iya barci don na rasa kannena uku

Matsalar sace 'yan makarantar dai ta kasance matsala da ta shafi kusan kowane gida a garin na Dapchi.

Na tarar da wata mata mai shekaru 25 mai suna Aisha Isa Kalallawa, a gidansu suna jimani tare da iyayenta. Kannenta uku na cikin 'yan mata 110 da 'yan bindigar suka sace.

Rike da jaririnta, Aisha ta bayyana mani cewa ba su taba shiga tashin hankali irin wannan ba a gidansu. Babban abin damuwar shi ne rashin sanin halin da yaran ke ciki.

''Kafin na yi aure, bamu rabuwa da su. Har wurin kwananmu guda. A ko yaushe yanzu tunaninsu na ke yi, bani iya cin abinci kuma bani iya barci tun bayan faruwar wannan al'amari''

Da farko dai gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa an samo wasu daga cikin 'yan matan da aka sace amma daga bisani sai ta nemi afuwa tana cewa bayanan da aka bata da farko ba gaskiya ba ne.

Ta kara da cewa: ''Wannan yanayi na rudani ya kafa jefa mu cikin bakin ciki. Yanzu duk bayanin da aka bamu, ko muka ji, ba mu yarda, sai mun ga yaran da idonmu.''

Image caption Iyayen Zahra sun ce tana da kokari sosai

Aisha ta kuma nuna damuwa kan halin da yaran ke ciki musamman kasancewarsu 'yan mata. 'Ni mace ce na san yadda rayuwar mace take. Yanzu sun tafi babu tufafi sai na jikinsu. Wannan ai wahala ce.''

Duk da irin wannan yanayi, tana fatan wata rana za ta ga 'yan uwan nata.

Yaro cikin 'yan mata

Yayin da ake ci gaba da nuna jimani kan harin da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kai inda suka sace dalibai a makarantar ta 'yan-mata zalla, bayanai na ci gaba da fitowa fili kan harin.

Ko da yake rahotanni sun bayyana cewa dukkan dukkan wadanda aka sacen mata ne, sabbin bayanai na cewa 'yan Boko Haram din sun kuma yi awon gaba da wani yaro mai suna Mala mai shekara 13 a lokacin satar dimbin mutanen.

Kakan yaron, Bukar Lawal Shanshani, ya shaida wa BBC cewa a lokacin da aka kai harin a makarantar ta 'yan mata, shi da yaron suna masallaci a rukunin dakunan kwanan malamai na makarantar.

Bayan da suka firgita suka watse, daga bisani sai yaron ya ce zai koma domin dauko takalminsa da ya bari a masallacin. Tun daga nan babu shi, babu duriyarsa.

Kakan yaron, ya ce dama mahaifin yaron malami ne a makarantar ta Kimiya da Fasaha ta 'yan-Mata da ke garin Dapchi.

''Muna jin 'yan Boko Haram din sun tafi da yaron tare da 'yan matan'' in ji Malam Bukar Shanshani.

Mazaunin garin na Dapchi ya kara da cewa sun kwashe tsawon dare suna Neman yaron amma har gari ya waye ba su same shi ba, daga nan ne jikinsu ya yi sanyi, suka fara tunanin cewa shi ma 'yan bindigar sun yi awon gaba da shi a harin na rånar Litinin 12 ga watan Faburairu, 2018.

Kamar sauran iyaye da dangin wadanda aka sace a garin na Dapchi. Ya bayyana fatan za a samo dukkan wadanda aka sace, yana mai kira ga hukumomi da su kara himmma domin ceto su.

Wannan ne dai karon farko da ake samu labarin cewa mai yiwuwa akwai namiji a cikin mutanen da maharan sun sace.

A halin da ake ciki dai, Kwalejin ta 'yan-mata zalla na ci gaba da kasancewa a rufe; babu dalibai, babu malamai sai takalma da sauran komatsan da daliban suka watsar a yayin da sukje gudun neman tsira.

A wajen makarantar a kan titi kuwa, an kafa wurin binciken matafiya inda aka girke sojoji bayan faruwar lamarin na satar 'yan mata.

Hukumomin Najeriya dai na cewa suna ci gaba da kokarin nemo yaran da aka sace inda aka tura jami'an tsaro da jiragen yaki.

To amma kawo yanz babu duriyarsu. Hakazalika, kungiyar Boko Haram wacce ake zargi da kai hari a makarantar, ba ta ce komai ba kawo yanzu.