Likita ya yi kuskure wajen tiyatar kwakwalwa

tiyata Hakkin mallakar hoto Getty Images

An dakatar da wani likita daga aiki a Kenya bayan da ya yi kuskuren fede kan mara lafiyar da ba shi ya kamata a yi wa tiyata a kwakwalwa ba.

Jaridar Daily Nation ta kasar ta ruwaito cewa daya mara lafiyar yana bukatar a yi masa aiki a kwakwalwa ne don cire masa daskararren jini, yayin da daya mara lafiyar kuma ke bukatar karamar kulawa ne kawai sbaoda kumburin da kansa ya yi.

Amma jaridar ta ci ga a da cewa 'sai aka samu akasi wajen sanya sunayen mara lafiyar a jikinsu, wanda hakan ya sa aka shiga da daya mara lafiyar da ba ya bukatar babban aiki a matsayin wanda za a yi wa aikin kwakwalwa.'

Likitocin ba su fahimci kuskuren da aka yi ba, har sai da aka shafe wasu sa'o'i a dakin tiyatar, a lokacin da suka fahimci cewa babu daskararren jini a kwakwalwar mutumin.

Babban asibitin Kenyatta ya ce ya yi matukar da-na-sanin abun da ya faru na wannan kuskure, aka kuma dakatar da likitan, in ji jaridar Standard.

Amma abokan aikin likitan sun nuna adawa da dakatarwar da aka yi masa, in ji Jaridar The Star, suna masu cewa wanda ya yi kuskuren sanya sunayen ya kamata a hukunta.

Jaridar The Nation ta ci gaba da cewa dukkan marasa lafiyar biyu suna cikin halin lafiya. Kuma wanda ke fama da matsalar daskararren jinin ba lallai a yi masa tiyata ba, bayan da aka ga cewa yana samun sauki sosai.

Labarai masu alaka