An kashe ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Nigeria

Borno Hakkin mallakar hoto OCHA
Image caption Boko Haram ta kashe Jami'an agaji uku da 'yan gudun hijira da dama a garin Rann

Wasu ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya guda uku sun rasa rayukansu a yayin da masu tayar da kayar baya suka kai hari wani sansanin sojoji da ke garin Rann a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato mai magana da yawun MDD tana mai tabbatar da afkuwar lamarin.

Ta kuma ce akwai wani karin jami'in da mai yiwuwa shi ma ya mutu, sannan kuma an sace wani ma'aikacin MDD din..

Ta kara da cewa dukkan wadanda aka kashe din 'yan Najeriya ne da ke aiki da MDD.

Wata majiya ta MDD ta shaida wa Rueters cewa maharan 'yan kungiyar Boko Haram ne, wadda ke kai hare-hare a yankin.

Ko a makon da ya gabata ma mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari wata makarantar sakandaren 'yan mata da ke jihar Yobe mai makwabtaka da Borno, inda ta sace 'yan mata fiye da 100, kuma har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

A watan Janairun 2017 ne wasu sojojin yaki suka kai harin sama bisa kuskure wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kauyen Rann, inda kusan mutum 115 suka mutu.