'Yadda 'yan Boko Haram suka sace kawayena a Dapchi'

'Yadda 'yan Boko Haram suka sace kawayena a Dapchi'

Tun bayan sace 'yan matan makarantar sakandare a garin Dapchi da ke jihar Yobe, al'amura suka sauya a garin, inda iyaye da 'yan uwa ke cikin zullumin halin da 'ya'yansu suke ciki.

Wasu iyaye da dalibai sun bayyanawa BBC yadda suke ji da sace 'ya'yansu da abokan karatunsu 110.

Lamarin dai ya yi kama da abinda ya faru a Chibok a 2014 inda har yanzu aka kasa gano sama da 'yan mata 100.