MSF ta dakatar da ayyukanta a Rann

Fiye da shekara guda ke nan da kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontiers ke aiki a garin Rann na jihar Borno Hakkin mallakar hoto OCHA
Image caption Fiye da shekara guda ke nan da kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontiers ke aiki a garin Rann na jihar Borno

Sakamakon wani hari da aka kai kan wani sansanin soji da ke garin Rann a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya a ranar Alhamis , kungiyar agaji ta Médecins Sans Frontières, ta dakatar da ayyukanta a garin tare da kwashe sauran jami'anta 22.

Har yanzu ba bu tabbas a kan adadin mutanen da suka rasa ransu da kuma wadanda suka jikkata sakamakon harin, to amma kafin kungiyar ta kwashe jami'an nata, sai da ta yi wa mutum tara magani wadanda suka samu raunuka sakamakon harin.

Kimanin mutum dubu 40 ne ke zaune a garin na Rann, kuma dukkan wadannan mutane sun raja'a ne a kan ayyukan wannan kungiyar wajen kula da lafiyarsu.

Kungiyar agajin cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, mafi yawancin wadanda ke zaune a garin sun samu mafaka ne bayan da suka bar gidajensu saboda yanayin zaman dar-dar din da ake ciki a yankunansu.

Babbar jami'ar kungiyar a Najeriya, Kerri Ann Kelly, ta ce "Mun dauki mataki marar dadi mai kuma ciwo saboda mun bar marassa lafiyar da muke kula da su cikin mutanen da ke zaune a Rann din da suka hada da yara 60 da muke kula da su a karkashin shirinmu na smaar da abinci mai gina jiki".

Jami'ar ta ce zasu dawosu ci gaba da ayyukansu a garin, da zarar sunga yadda yanayin tsaro ya canja.

An kashe ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Nigeria

An kai wa kungiyar agaji ta Save the Children hari

Harin da aka kai na baya-bayan ya nuna cewa al'ummar jihar Borno su wannan rikici da ake fama da shi a yankin ke shafa.

Saboda suna cikin wani yanayi da rayuwarsu ta koma kacokan a kan bukatar taimako musamman daga kasashen waje domin su tsira da rayuwarsu.

Kungiyar agaji ta Médecins Sans Frontières, ta fara bayar da taimako a bangaren lafiya a garin Rann tun a watan Janairun shekarar 2017.

Kungiyar ta na taimaka wa mutane wajen maganin cutuka kamar na Zazzabin cizon sauro wato malaria da kula da masu matsalar rashin abinci mai gina jiki da dai sauran cutuka da suka shafi zama a wurare marassa kyau.

Labarai masu alaka