An fara gwajin sabuwar allurar riga kafin zazzabin Typhoid

Hukumar lafiya ta duniya ta amince da sabuwar allurar rigakafin. Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Hukumar lafiya ta duniya ta amince da sabuwar allurar rigakafin.

Ana gwajin wata sabuwar allurar rigakafi kan cutar zazzabin taifod akan yara kanana a wani asibiti da ke kasar Malawi.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta amince da sabuwar allurar rigakafin.

An kuma yi kiyasin cewa cutar taifod ta addabi mutane miliyan 12 zuwa 20 a kasashen duniya musamman a kudancin Asiya da yankin Africa kudu da sahara.

Za a fara riga-kafin malaria a Ghana da Kenya da Malawi

'Buhun masara ne ya cece ni a Malawi

Malawi: Ana kubutar da giwaye