Adikon zamani kan soyayya a aure: Wajibi ko sakaci?

Ku latsa alamar lasifika domin sauraren cikakken shirin:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Soyayya a Aure: Wajibi ko sakaci?

Mata da dama na kokawa kan gushewar soyayya a rayuwar aurensu sabanin kafin auren.

Da zarar an gama angwanci da amarci, sai a koma ga aikin gida na yau da kullum. Babu wani romon soyayya kamar a can baya da ake shaukin juna.

Wasu na ganin akwai sabanin fahimta kan batun nuna tsagwaron soyayya a arewacin Najeriya. Wasu da dama na ganin nuna wa mata so a fili ba shi ba ne soyayya. Sai dai kuma ana ganin nuna kauna da soyayya na da matukar tasiri ga jin dadin rayuwar aure.

Wasu Maza na ganin nuna kauna da furta kalaman soyayya ga matansu kamar kayar da girma ne a matsayinsu na "Mai Gida".

Kamar yadda wasu ke ganin nuna soyayya zai kawo raini tsakaninsu da matansu.

Amma akwai hujjoji da dama da suka nuna cewa ma'auratan da ke nuna kaunar juna da kulawa ko dai ta hanyar kalamai ko cudanya zai kasance sun fahimci juna da samun alaka mai karfi.

Ina ganin ba zai zama laifi ba idan kun gwada.

Labarai masu alaka