Nigeria: Matar wakilin VOA da dansa sun kubuta

Kaduna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matsalar garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a Najeriya

'Yan bindiga sun sako matar wakilin kafar yada labarai ta VOA da dansa da suka sace a Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce an sako matar wakilin na VOA, Nasir Birnin Yaro, da dansa ne bayan an biya diyyar N2m.

A makon jiya ne aka sace mutanen biyu.

Maharan sun kashe wani jami'in hukumar kiyaye hadurra ta FRSC da suke makwabtaka da Nasir Birnin Yaro.

Birnin Yaro ya tabbatar wa da wakilin BBC Nura Muhammad Ringim da sakin iyalin nasa.

Da tsakar dare ranar 28 ga watan Fabrairu ne 'yan bindigar suka kutsa gidan dan jaridar.

Ya ce lokacin da suka shiga gidansa da ke Birnin Yaro, ba ya nan amma sun iske iyalinsa suna tambayar matarsa inda yake.

A lokacin ne kuma suka harbe makwabcinsa Sabitu Abdulhamid, wani jami'in hukumar kiyaye hadurra bayan ya shiga gidan da nufin taimaka wa iyalinsa.

Bayan sun kashe shi ne suka tafi da matar da dansa.

Birnin Yaro ya ce yana tunanin sun shigo gidansa ne da nufin su yi garkuwa da shi, amma da ba su same shi ba suka tafi da iyalinsa.

Kaduna dai na cikin yankunan arewacin Najeriya da ke fama da matsalar sace-sacen mutane kuma matsala ce da ta ki ci ta ki cinyewa.

Labarai masu alaka