Kun taba ganin mutumin da ke 'tafiya a kan iska'?

Prophet Sherpherd Bushiri

An rika tafi da rawa da tsalle lokacin da yake kan hanyarsa ta shiga zauren, tare da masu tsaron lafiyarsa.

Irin halin da masu bauta ke shiga ciki ke nan - cikinsu har da wadanda kan yi jiran fiye da awa biyar ba tare da sun kosa ba - domin su sanya shi a idanunsu. Wasu ma har faduwa suke yi saboda gajiya da tsayuwa.

Amma, me ya sa ba za a yi jiran ganinsa ba? Wannan shi ne mutumin da ya warkar da masu cutar HIV, ya dawo wa da makafi ganinsu, ya sa talakawa suka zama masu arziki, sannan ya taba 'yin yawo a kan iska'.

'Annabi' Shepherd Bushiri ya girma ne a kauyen Mzuzu da ke arewacin Malawi.

A halin da ake ciki, dubban mutane ne ke halartar filayen wasa domin sauraren hudubarsa - cikin mabiyansa akwai wadanda za su iya binsa kowacce kasa domin su yi tozali da shi.

Hakkin mallakar hoto Ecg ministries
Image caption A jajiberen sabuwar shekara mabiyansa sun cika makil a filin wasan da ke daukar mutum 95,000 wanda ke Johannesburg

Mutane kan ziyarce shi daga Amurka da Burtaniya da kasashen Asiya a kai-a kai - hasalima a yanzu akan karkada tutoci a zauren cocin Enlightened Christian Gathering (ECG) Ministries inda yake yin wa'azi.

Na hadu da wannan mutum da ake kira "Major One" a cocinsa da ke Pretoria, babban birnin Afirka ta Kudu.

An ba mu damar shiga cikin cocin, wacce aka kawata da jajayen igiya da darduma inda masu tsaron lafiyarsa suka yi kuri gefe da gefe.

Warkar da maras lafiya

Mai wa'azin cocin dan kimanin shekara 30 na sane da zarge-zargen da ake yi masa cewa shi dan damfara ne, sai dai ya yi watsi da su.

Ya shaida min cewa "Cocina ba ta kowanne irin mutum ba ce, ta mutanen da suka yi imani ce. Ni annabi ne da Allah ya aiko domin yin aikinsa. Allah yana bai wa mutane sauki a cocina."

"Akwai lokacin da na gaya wa likitoci su zo min da mutanen da ke dauke da cutar HIV a nan Pretoria - sun yi musu gwajin da ya nuna suna dauke da kwayar cutar ta HIV, kuma daga nan ne na yi musu addu'a sannan na ci gaba da yi musu addu' kuma yanzu sun warke."

Wane ne Shepherd Bushiri?

Hakkin mallakar hoto ECG Ministries
  • Mai wa'azincoci ne da aka haifa a kasar Malawi wanda ke da coci a Ghana da Afirkaa ta Kudu
  • Rahotanni sun ce gwamnatin Botswana ta hana shi wa'azi a kasar saboda ilhamar da yake yi ta samun "kudi"
  • Ya yi ikirarin warkar da masu HIV
  • Wani hoton bidiyo da aka rika watsawa a shafukan intanet ya nuna shi yana tafiya 'a kan iska'
  • Yana da jiragen sama na kasaita hudu

A wajen dakin da muka shiga, mabiyansa sun yarda da duk abin da ya ce. Sun yarda cewa yana da mu'ujizar warkar da marasa lafiya da kuma fitar da su daga cikin talauci.

"Ilhamar da annabinmu kuma ubanmu [Prophet Bushiri] ke koyarwa a kowanne mako na da matukar ban mamaki," in ji Xolani Msibi dan shekara 24.

Ya kara da cewa Bushiri ya warkar da 'yar uwarsa wacce ta yi fama da cutar rashin iya tafiya "ba tare da ya dora ko da hannunsa a kanta ba".

"Na dade ina fafutikar neman aiki ban samu ba amma bayan na zo nan na tafi sai da na samu aiki biyu, wadanda sai da na zaba na darje."

Ba a kasar Afirka ta kudu ko ma nahiyar Afirka kadai aka yarda da mu'ujizar Prophet Bushiri- har da kasashen duniya daban-daban.

Ciki har da malamin cocin nan dan kasar Isra'ila da ke zaune a Amurka, Benny Hinn, da mai wa'azin kasar Jamus Rienhard Bonnke da dai sauransu.

Duk da yake addinin kirista ya shafe shekara da shekaru a Afirka, mutane da dama sun yi amannar cewa sauye-sauyen da aka samu a yanzu na da alaka da wasu kungiyoyi na kasashen waje.

A duk ranar Lahadi, fiye da mutane 40,000 ne halartar cocin Bushiri domin sauraren wa'azinsa sannan su sayi magunguna da sauran abubuwan yau da kullum da ake sayar wa a harabar cocin wadanda suka hada da "mai na ilhama", kalanda, agoguna da takardar share bayan-gida ta musamman, hulunan da ke dauke da hotonsa.

Ana nuna fargaba kan irin wadannan masu wa'azi a Afirka ta kudu, sai dai abin da hukumomi ba sa so a zarge su da aikatawa shi ne: yin kafar ungulu ga 'manzanni Allah.'

Image caption "Man da ke da ilhama" dauke da hoton mai wa'azin
Hakkin mallakar hoto Ecg ministries
Image caption Ya ce bai kamata masu wa'azi su rika shiga irin ta talakawa ba
Hakkin mallakar hoto Ecg ministries

Labarai masu alaka