Sabon rikici ya barke a Taraba

An kona gidaje a sabon rikicin da ya barke a Mambila Hakkin mallakar hoto Also Salisu
Image caption An kona gidaje a sabon rikicin da ya barke a Mambila

Rahotanni daga yankin Mabila a jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya, sun ce an samu asarar rayuka da kuma ta dukiya a tashin hankalin baya-bayan nan tsakanin fulani makiyaya da kuma 'yan kabilar Mambila.

Rahotannin sun ce, rikicin ya barke ne a ranar Alhamis da ta wuce sai dai har yanzu kura bata lafa ba.

Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, shi ne dan majalisar dattawa mai wakiltar Taraba ta tsakiya, ya shaida wa BBC cewa, rikicin ya barke ne a garuruwan Kakara da kuma Yerimaro.

Sanatan ya ce, an an farwa wasu makiyaye ne da dai sauransu.

Alhaji Yusuf Abubakar, ya ce rahotannin da suka samu sun nuna cewa, rikicin ya barke ne tsakanin fulani makiyaya da kuma 'yan kabilar Mambila.

Sanatan ya ce har yanzu kura bata lafaba domin ana kashe dabbobi, kuma wuraren da ake rikicin ba wurare ne da za a yi musu shigar sauri ba dole sai an shirya.

Alh. Yusuf ya ce, jami'an tsaron da suke a Mambila ba su da yawa, amma yanzu ya nemi da a kara tura jami'an tsaro yankunan da ake wannan rikici domin a kwantar da hankali.

Sanatan ya ce, a rikicin na baya-bayan nan an yi asarar rayuka da dukiya domin an kona gidaje da dama, amma kuma ba zai iya fadin adadin wadanda suka mutu ko jikkata ba a yanzu, sai nan gaba idan ya samu cikakken bayani daga mahukuntan jihar ta Taraba.

A watan Yunin da ya gabata ma dai an samu irin wannan rikici inda har kungiyar fulani ta Miyetti Allah ta yi zargin cewa an kashe fulani sama da 800 a wani hari da aka kai musu garin na Mambila.

Wasu dai na ganin cewa, ana ci gaba da samun rikicin ne saboda rashin daukar mataki a kan mutanen da ake zargi da haddasa rikicin.

Labarai masu alaka