Kankana ta kashe mutane a Australia

Kankana mai dauke da kwayar bacteria ta kashe mutane a Australia Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kankana mai dauke da kwayar bacteria ta kashe mutane a Australia

Mutum uku sun mutu a Australia bayan da suka ci wata gurbatacciyar kankana mai dauke da kwayar bacteria.

Wasu tsofaffi 15 kuma yanzu haka na kwance a asibiti bayan da suma suka yi amfani da kankanar.

Mutane biyu na farko da suka mutu bayan sun ci kankanar, sun fito ne daga jihar New South Wales, yayin da mutum na ukun kuma ya fito daga jihar Victoria duk a kasar ta Australia.

Yanzu haka dai hukumomin lafiya a kasar sun gargadi tsofaffi da mata masu juna biyu da kuma yara game da cin kankana musamman wacce aka yayyanka.

Mutum 15 din da yanzu ke kwance a asibiti an gano cewa sun samu kwayar cuta ne sakamakon cin gurbatacciyar kankanar.

An dai gano cewa ana samar da gurbatacciyar kankanar ne daga wata gona da ke kusa da wani gari mai suna Griffith a jihar ta New South Wales.

Tuni dai aka haramta sayar da kankana a manyan shagunan kasar bayan barkewar wannan cuta sakamakon amfani da gurbatacciyar kankana a kasar.

Labarai masu alaka