Wani nau'in nama na kisa a Afirka ta Kudu

An yi gargadin cin duk wani nau'in nama da aka sarrafa a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An yi gargadin cin duk wani nau'in nama da aka sarrafa a Afirka ta Kudu

Manyan shaguna a Afirka ta Kudu sun fara kiran da a dawo da naman da aka saya a wajensu bayan da aka gano cewa naman ne musabbabin wata cuta da ta barke wadda kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 180 a kasar.

Ministan lafiya na kasar ya ce, an gano cutar ne a cikin wani nama da aka sarrafa shi wanda mallakar wani kamfani ne na RCL Foods.

Kusan mutum dubu guda ne suka kamu da wannan cuta a kasar a cikin shekara guda.

Majalisar dinkin duniya ta ce tayi amanna cewa barkewar wannan cuta ita ce mafi girma a duniya.

Alamomin cutar dai sun hada zafin jiki da amai da gudawa.

An dai yi amanna cewa cutar tana da matukar hadarin gaske.

Yanzu haka dai shagunan kasar na ta gaggawar kwashe sarrafaffan naman da suka ajiye a kantocin da ke shagunansu, musamman nau'in naman da aka fi sani da Polony wanda aka gano cewa shi ne ya haddasa barkewar wannan cuta.

Domin gudun yaduwar cutar,mahukunta a kasar ta Afurka ta Kudu sun gargadi mutane akan cin naman da aka sarrafa wanda baya bukatar dahuwa.