Rayuwar mata: An ci gaba ko da sauran rina a kaba?

Rahma Abdulmajid Hakkin mallakar hoto Rahma Abdulmajid
Image caption Rahma Abdulmajid na ganin ba a yi ci gaban a zo a gani ba a gwagwarmayar kwato hakkin mata

Rahma Abdulmajid Rahma Abdulmajid ce ta rubuta wannan makala

"Babu wani a duniya ko a tarihi da ya taba samun 'yancinsa muddin zai nema ne a hannun masu take masa hakki."

Wadannan kalaman Assata Shakur ne, wadanda ta furta a kan ilahirin 'yanci, amma kalaman sun fi aiki a kan 'yanci da ci gaban mata a duniya wadanda ke tafiyar hawainiya.

Duk kuwa da an samu abin da ba a rasa ba wajen ci gaban matan a wasu fannoni na lafiya da ilmi ko auratayya, musamman ma a yankunan da ke makwabtaka da Afirka kamar Turai da wasu sassan Asiya mai gafaka, amma kwalliya ba ta ma ga sabulu ba ballantana ta biya shi hakkinsa.

Za mu ankara da hakan ne idan muka yi nisan zango a waiwaiye kan menene kason mata a duniyar da takwarorinsu maza suka yi wa babakere.

Kusan a duk tsayin tarihin mace, kasonta a duniya bai wuce na wasu abubuwa da ba za a iya kwace mata su ba, ko kuma ko da an kwace din wanda ya karba wahala zai sha.

Wadannan abubuwa su ne abin da ya shafi jima`i, da haihuwar yara, da kula da ayyukan gida wadanda suka hada da shara, da wanke-wanke da kula da yara.

Sannan ko a wannan kaso, wanda kusan saboda shi ne kadai aka hakura ake haihuwarta zuwa yanzu, maza ba su gama amincewa da ba mace wuka da nama a wannan lamari ba, don su ne ke da zabin suna da ilahirin umarni a kan abin da ta haifa, kamar yadda bukatarsu a yayin jima`i ke sama da tata. Kai! Har ma a abin da za ta dafa su ne masu cewa yau shinkafa za a ci gobe tuwo.

Sai dai ko a wadannan fannoni wadanda aka mayar da su killataccen aikin mata, matan ba su sarara ba, domin bincike ya nuna cewa rabon matan da jiya-i-yau a kan harkar haihuwa da jima`i da girki kadan ne ci gaban da aka samu, inda har yanzu rahotanni ke nuna cewa mata na fuskantar cin zarafi mafi girma a fadin duniya a wadannan bangarori.

Hakkin mallakar hoto Un Women
Image caption Wasu daga cikin matan da ke gwagwarmayar nema wa sauran mata 'yanci

A bangaren jima'i

•Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa daya a cikin duk mata goma a duniya — adadin da jimilla ya haura mata miliyan 120 — na fuskantar tursasawa wajen jima'i ko ma fyade kai-tsaye daga mazajen da suka taba aura, ko suke aure, ko ma samarinsu.

Ban da sama da mata miliyan 750 wato hudu a cikin duk mace shida na duniya da ke fuskantar auren wuri ba tare da sun kai shekarun da za su iya zaben abokin zama ba. Wannan lissafi ya lashe sama da rabinsa a kasashen Afirka masu tasowa.

•Wasu alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a kan zamantakewa dangin aure da soyayya ta yi nuni da cewa sama da kashi 35 cikin dari na ilahirin matan duniya na fama da rikici ko barazana ta kai-tsaye ko a fake daga abokan zamantakewarsu na aure ko soyayya wadanda maza ne.

Wani binciken ma ya bayar da kididdigar da ta haura wadannan alkaluma ta kai su kashi 70 cikin dari na matan da suka isa aure ko suke cikin rayuwar auratayya na fuskantar irin wannan barazana a wasu lokuta na rayuwarsu, lamarin da kan sanya matan fuskantar matsaloli kamar zubewar ciki, da hawan jini, da HIV, da ma rasa rayuka fiye da tsirarun matan da ba sa fuskantar irin wannan barazana.

Wani rahoto mai alaka da wannan ya yi nuni da cewa kusan ilahirin matan da suka rasa rayukansu a fadin duniya a shekarar 2012 ta hanyar kisa, sun rasu ne sakamakon kisa kai-tsaye ko kisan mummuke daga abokan zamansu maza, sabanin maza wadanda kashi shida ne a cikin dari suka rasa rayukansu a dalilin abokan zamansu mata.

Bangaren haihuwa

•Shi ma wannan bangaren maza na taka rawa wajen samar wa mata matsaloli wadanda suka hada da auren wuri da ke janyo haihuwar wuri mai matsaloli, da ma hana kayyade iyakar abubuwan da za a haifa, ko cuzgunawa matan yayin daukar ciki.

Wannan al'amari yana ci gaba da janyo mutuwar miliyoyin mata a yayin da suke dauke da juna biyu ko kuma haihuwar tauyayyiyar halitta ko ma rasa cikin baki daya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Har yanzu ana samun yawan mace-macen mata wajen haihuwa

Bangaren ayyukan gida

•Matsalolin da mata suke fuskanta a aikin gida ya faro daga rikidewar ayyukan gidan daga wata al`ada da mata suke so zuwa wata bauta wadda ta wajaba a kansu a ciki da wajen gidajensu.

Ban da alkalumman mutuwar aure da ke karuwa a dalilin kananan ayyukan gida da mace kan samu tangarda wajen aiwatarwa kamar kai ruwan wanka, ko shara, ko zambada magi kafi-zabo a miyar kukar da ta kan kada a gidajen aure — wanda ke cikin manyan dalilan da ke kashe sama da aure 700 a duk mako a jihar Kano ta arewacin Najeriya kadai, kamar yadda wata kididdigar Hukumar Hizba ta nuna — abin ya tsallaka zuwa safarar mata daga gidajensu ko na iyayensu zuwa kasashen da aka fi samun kudaden shiga don yin irin wannan bauta ta babu gaira babu dalili, inda abin takaici akasarin matan aure kan yi irin wannan aikatau ne bayan da mazajen aurensu ko 'yan uwansu maza suka kai su domin karbar kudin ba matan ne za su yi amfani da shi ba.

Misalin irin wannan shi ne labarin Karla Jacinto wadda ta yi hira da tashar talabijin ta CNN inda ta zayyana mummunan labarinta na yadda ake yi mata fyade sau 30 a duk rana har sai da adadin fyaden da aka yi mata ya kai 43,200, sanadiyyar dadin bakin namijin da ya zamo saurayinta.

Wata kididdiga da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Amurka ta fitar ta nuna cewa kashi 80 cikin dari na mutane 800,000 da aka tsallako da su zuwa kasar ta Amurka kadai mata ne da yara kanana, ban da wata kididdiga ta Hukumar Kwadago Ta Duniya, wadda ke nuna cewa akalla a cikin bayi miliyan 20 da aka yi safara sama da miliyan 11 mata ne.

Wannan a bangaren da ya shafi abubuwan da ake ganin tilashin mata ne ke nan. Kada a tabo abubuwan da duniya ke kallo a matsayin kyauta ce za a yi wa mace ba don ya zamo hakkinta ba kamar su ilimi, da damar sana`a ko aikin gwamnati, ko rike wani mukami da sauransu.

A wannan bangaren har yau nasarar ba ta wuce ta karuwar kururuwar muryoyi a kan dacewar a bai wa mace irin wannan dama ba.

Sai kuma musayar yawu a tsakanin wadanda ke ganin cewa za a iya yi mata irin wannan kyauta ko babu bukatar yi mata, amma muryoyin da za su ce dama can hakkinta ne, zan iya cewa ba a fara jinsu ba ma a akasarin yankunan yammaci da kudancin Afirka inda har UNESCO ta fitar da kididdigar da ke nuna cewa a Najeriya kadai, inda a ke ganin an samu ci gaba ta bangaren ilmi, kashi hudu ne cikin dari na 'ya'yan masu karamin karfi ke tsallake yaki da jahilci wanda ke nuna cewa lallai talauci ya taka rawa a kan ko mace ta dace ta yi karatu ko a'a.

Ke nan idan haka ne har yau ana ci gaba da amanna cewa ilimi wani abinci ne da sai maza sun ci sun koshi mata za su iya samun sudi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Har yanzu akwai wawakeken gibi tsakanin ilimin mata da na maza musamman a Afirka

Wani hasashe mafi takaici shi ne rawar da mabiya addinai kan taka wajen kekasa kasa a kan ganin cewa mata ba su samu 'yanci ba ta hanyar amfani da abin da mabiyan suka yi imani ta barauniyar hanya.

Ga misali Musulunci, wanda aka yi amanna da cewa shi ne addinin sama na farko da ya yi kira ga dorewar hakkokin mace, mabiyansa kusan sun zamo su ne sahun karshe wajen amincewa da 'yancin mace, wanda hakan na nuna a fakaice sun bijirewa kiran addinin nasu wanda suke nuna biyayya gare shi ido rufe.

Yawan Musulmi da kuma rawar da suke takawa wajen amfani da bahaguwar fahimtar addini wajen take hakkin mata abu ne da duniya za ta iya yakarsa da gaske.

Bana raba daya biyu a kan cewa mata za su samu biyan sama da kashi 40 cikin dari na bukatunsu idan aka yi la'akari da girman hakkokin da wasu Musulman ke amfani da addini wajen danne musu, wadanda suka hada da hakkokin aure da saki da haihuwa da ilimi da rike mukamai da kuma ayyukan ofis ko sana'a.

Ko da yake har fannin amfani da addini wajen take hakkokin mata da Musulmi ke jagoranta a duniyar yau an fara samun sauyi, inda kiraye-kiraye ke kara kamari wajen fayyace matsayar Musulunci a kan hakkokin mata da matsayin Musulmi wajen amfani da wannan hakkoki.

Karamin misali shi ne yadda a Masautar Kano shekaru fiye da 60 da suka shude aka taba samun wani sarki da fadarsa ta fitar da fatawa karkashin addinin musulunci ta hana mata karbar gadon gidajen iyayensu inda wasu ke tashi da gadon bishiyar kuka a tsakar gidan babbar fadar da mahaifansu suka mutu suka bar musu don kawai mata ne, duk kuwa da kiran da aya ta yi karara a Alqur`ani mai tsarki na a ba su gado.

Amma yanzu haka an samu wani sarkin wanda ke kira da a tabbatar da hakkokin mata ba ma kawai na gado ba har ma da na auratayya, da ilimi, da aikin yi, kuma shi ma kiran nasa dai a cikin musulunci ne wanda yake sarauta a karkashinsa.

Hakan manuniya ce a kan cewa lallai addini wani abu ne da mutane kan yi amfani da shi ko dai ya yi aiki a kansu ko kuma su yi aiki a kansa ta bangaren al'adu ko bukatunsu.

Wani abu da za mu zura ido mu gani shi ne abin da wannan shekara ta 2018 ta tanadar wa mata na game da hakkoki da 'yancin walwala — za a samu ci gaban a-zo-a-gani ko a'a.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Labarai masu alaka