Allunan maraba da Yusuf Buhari sun harzuka 'yan Nigeria

Nigerian govt Hakkin mallakar hoto Nigerian govt
Image caption Ministan lafiyar kasra ne ya tarye shi a lokacin da ya dawo

Wasu 'yan Najeriya sun harzuka da ganin allunan da aka sanya a tituna don yi wa dan shugaban kasar Yusuf Buhari maraba da dawowa daga jinya a kasar waje, bayan da ya yi hatsari a kan babur.

Daya daga cikin allunan, wanda aka kafa a babban birnin tarayyar kasar, Abuja, yana dauke ne da sako kamar haka: "Yaran Najeriya suna yi wa Allah godiya da Ya raya ka. Ko yaushe za mu kasance masu yi maka addu'a."

Wani allon kuwa an yi rubutu ne kamar haka: "Muna son ka Yaya Yusuf."

Hakkin mallakar hoto Twitter

Sai dai a yayin da wasu ke ganin sanya allunan ba wani abu ba ne, wasu kuwa cewa suke yi hakan bai kamata ba, musamman a lokacin da ake tsaka da jimamin sace 'yan matan makarantar sakandare fiye da 100 a garin Dapchi na jihar Yobe.

Hakkin mallakar hoto twitter

Wasu kuwa a shafinsu na Twitter cewa suka yi irin wannan halayya ba komai ba ce illa bambadanci.

A ranar 27 ga watan Fabrairu ne dan na Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga jinyar raunukan da ya yi sakamakon hadarin da ya yi.

Gabannin dawowar tasa da mako guda dai an yi rade-radin cewa ya mutu, amma daga bisani fadar shugaban kasar ta musanta hakan, inda ta ce yana kasar Jamus.

A farkon watan Janairu ne aka sallami dan shugaban kasar daga wani asibitin Abuja bayan hadarin da ya yi a watan Disamba.

Hatsarin ya faru ne a unguwar Gwarimpa da ke birnin da daren ranar Kirstimeti, kuma fadar shugaban kasar ta ce ya karye a kafa sannan ya yi rauni a kansa sakamakon hatsarin.

Labarai masu alaka