Nigeria: An kashe mutum 30 a Benue

Benue Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images

Akalla mutum talatin aka ruwaito an kashe a cikin jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya bayan wani rikici tsakanin fulani makiyaya da kuma manoma.

A ranar Litinin ne 'yan sanda suka gano gawar wata yarinya 'yar shekara 11 sanye da tufafinta na makaranta.

A ranar Juma'a za a gudanar da jana'izar bai-daya ta mamatan.

Kwararowar hamada da rikicin 'yan ta-da-kayar-baya a wani yanki na arewacin Nijeriya na tilastawa makiyaya wasunsu dauke da makamai matsawa zuwa kudancin kasar.

A baya-bayan nan ne, gwamatin jihar Benue ta kaddamar da dokar da ke wajabta killace dabbobi a jihar.

Sai dai wasu makiyaya sun yi biris, suna korafin cewa gwamnati ba ta cika alkawarinta na kebe wa dabbobinsu wuraren da za su yi kiyo ba.

Wannan na zuwa duk da shugaban 'yan sandan Najeriya ya koma Benue tare da wasu rundunonin 'yan sanda na musamman guda biyar domin tabbatar da tsaro da bin doka da oda.

Rikicin makiyaya da manoma dai ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a jihohin arewacin Najeriya.

Labarai masu alaka