Shugaban Koriya Ta Arewa ya gana da jami'an Koriya Ta Kudu

North Korean leader Kim Jong-un greets a member of the delegation of South Korea's president on March 6, 2018 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kim Jong-un ya tarbi bakin nasa na Kudu cike da annashuwa

Koriya Ta Kudu ta ce shugaban Koriya Ta Arewa, Kim Jong-un ya bayar da hasken cewa zai so hawa teburin tattaunawa a kan rabuwa da makaman nukiliya idan za a ba shi tabbacin tsaron kasarsa.

Koriya Ta Kudun ta ce an tattauna batun hakan ne a yayin da jami'anta suka gana da shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong-un a birnin Pyongyang a ranar Litinin.

Gwamnati a birnin Seoul ta kuma ce Koriya Ta Arewa a shirye take ta gudanar da tattaunawa da Amurka kuma tana iya dakatar da gwaje-gwajenta na makamai masu linzami da na nukiliya.

A can baya dai Koriya Ta Arewa ta sha karya alkawuran da take dauka na dakatar da shirin nukiliyarta.

Tun bayan hawansa mulki a shekara ta 2011, ba a taba sa ran Shugaba Kim zai iya barin kasarsa ba, ko kuma ya gana da shugaban wata kasa hatta ma China, kawa ta zahiri ga Koriya Ta Arewan ba.

A cikin watan gobe, Kim Jong-un zai yi wani taro da Shugaba Moon Jae-in a kan iyakar kasashen biyu mai tsananin tsaro.

Ganawar za ta zama ita ce ta farko da za su yi a cikin gomman shekaru.

Wannan al'amari ya zo ne sakamakon ganawa da Shugaban Koriya ta Arewa ya yi da wani ayarin jami'an Koriya Ta Kudu, wadanda komawarsu gida kenan daga birnin Pyongyang.

Wata sanarwa daga ofishin shugaban Koriya Ta Kudu ta ce: "Arewa ta nuna son dakatar da shirinta na nukiliya a yankin Koriya. Idan ake age barazanar soji da Arewan ke fuskanta aka kuma tabbatar mata da tsaronta, to ta ce ba ta da zabi illa janye aniyar tata.

Dama dai Amurka ta sha cewa za a hau teburin tattaunawa ne kawai idan Koriya Ta Arewan ta dakatar da shirin nukiliyar.

Shugaba Donald Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: "Duniya tana kallo kuma tana jira.!"

"Ko da ba da gaske ba ne, to Amurka a shirye take ta dau duk mtakin da ya dace."

Me ya faru a wajen ganawar Koriyoyin biyu?

Jami'an Koriya Ta Kudu sun yi liyafar cin abinci ta tsawon sa'a hudu tare da Shugaba Kim Jong-un a ranar Litinin.

Daga cikin tawagar akwai shugaban hukumar leken asiri na Kudun Suh Hoon da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaron kasa Chung Eui-yong.

Hotunan da suka dauka sun nuna Mr Kim da bakinsa na Kudu suna cike da fara'a a teburin cin abinci.

Haka kuma matar Mr Kim Ri Sol-ju, wadda ba ta faye bayyana a wuraren taruka ba, da kanwarsa Yo-jong, wadda da ita aka je Kudu lokacin gasar wasannin Olympics a watan da ya gabata.

Ga dukkan alamu dai kasashen biyu sun fara nuna alamun sasantawa da juna ne bayan kammala gasar Olympics, inda suka tsaya a karkashin tuta daya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ga dukkan alamu dai kasashen biyu sun fara nuna alamun sasantawa da juna ne bayan kammala gasar Olympics, inda suka tsaya a karkashin tuta daya.

Labarai masu alaka

Karin bayani