Abincin Banku ya hallaka mutane a Ghana

Banku da miyar kubewa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Banku da miyar kubewa

Hukumar tantance abinci da maguguna ta Ghana, ta tabbatar wa BBC mutuwar al`ajabi da wasu mutane biyar suka yi a wani kauyen jihar Volta, bayan cin daya daga cikin abincin kasar mafi shahara wato banku da miyar kubewa.

Hankulan mazauna kauyukan da ke jihar ya yi matukar tashi, saboda mutuwar da wasu mazauna daya daga cikin kauyukan su biyar suka yi.

Hukumar tantance abinci da magungunan ta ce, tana zargin masarar da aka yi amfani da ita wajen tuka bankun ce sanadiyyar mutuwar wadannan mutane bayan da suka ci bankun.

Yanzu haka dai, hukumar tace ta fara binciken kwa-kwaf don gano musabbabin mutuwar mutanen, yayin da mazauna kauyen da kewaye suke fargabar yaduwar wannan matsala.

Hukumar ta ce zata fara bincikenta ne ta hanyar gwajin samfurin abincin da mutanen suka ci domin ganin ingancinsa, sannan hukumar tsaro da kuma shugabannin gundumar da lamarin ya faru ma na da rawar da zasu taka wajen gano abinda ya haddasa mutuwar mutanen da kuma tabbatar da cewa ba a sake samun irin wannan matsala ba.

Labarai masu alaka