Miliyoyin mutane suna kada kuri'a a zaben Saliyo

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bidiyon yadda zaben Saliyo ke gudana

A ranar Laraba 7 ga watan Maris ne, al'ummar kasar Saliyo ke fita rumfunan zabe don zabar shugaban kasa da `yan majalisar dokoki.

Shugaba Earnest Bai Koroma, ya cinye zango biyu na mulkinsa, inda ya shafe shekara goma a kan karaga.

Mutum 16 ne ke takarar shugabancin kasar, ciki har da mata biyu.

Wannan zabe dai a cewar masu lura da al`amura shi ne mafi rubibi idan aka yi la'akari da yadda ya cika ya batse da `yan takarar shugabancin kasa 16, wadanda kuma ake ganin cewa akalla kashi daya cikin hudun `yan takarar suna da yankunan da suka yi kaka-gida a siyasar Saliyo.

Shugaba mai ci Earnest Bai Koroma, na jam`iyyar APC mai mulki dai na goyon bayan Dr Samura Kamara, wato tsohon Ministan harkokin wajen gwamnatinsa na jam'iyyarsa.

Ita kuwa babbar jam`iyyar adawar kasar, wato SLPP, tsohon shugaban kasar na mulkin soji, wato Birgidiya-Janar Julius Mada Bio, ta tsayar a matsayin dan takararta.

Sai kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Saliyo, wato Samuel Sam Sumana, wanda suka yi baram-baram da shugaba Bai Koroma har aka tsige shi daga mukaminsa, wanda yanzu ya tsaya takarar shugabancin kasa a tutar jam`iyyar Coalition for Change.

Femi Cole, ita ce daya daga cikin mata biyun da suka tsaya takarar shugabancin kasar, inda ta kafa tata jam`iyyar mai suna Unity Party, yayin da takwararta, Jemba Gbandi, ke takara a jam`iyyar RUF, wato Revolutionary United Front, jam`iyyar da ke da alaka da wasu sojojin tawaye tun zamanin yakin basasa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutum miliyan uku ne ake sa ran za su kada kuri'unsu a Saliyo a zaben bana

'Yan takara takwas ne dai aka fi jin amonsu a tsakanin mutum 16 da ke zawarcin kujerar shugaban kasa a Saliyo.

Baya ga zaben shugaban kasa, kazalika a ranar Larabar ne za a yi zaben `yan majalisar dokoki, inda 112 za su jarraba farin jininsu a rumfunan zabe, yayin da 12 za su samu kujerun ne ta hanyar nadi.

Mutum miliyan uku ne ake sa ran za su fita kada kuri`a a rumfunan zabe fiye da dubu 11, daga cikin al`ummar kasar mai yawan mutum miliyan bakwai da doriya.

Hukumar zaben kasar dai ta bayyana cewa ta shirya wa zaben, kuma kayan aiki ya kai ko`ina.

Kungiyoyin farar-hula sun kwashe lokaci suna ta nasiha a kan illar tada fitina a lokacin zabe.

Labarai masu alaka