Ana fama da matsanancin fari a Somalia

Mutane na bukatar taimakon abinci da sauran kayan bukatun yau da kullum a Somalia Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane na bukatar taimakon abinci da sauran kayan bukatun yau da kullum a Somalia

Ana gargadin samun gagarumin rikici a Somaliya, saboda farin da aka jima ana fama dashi a kasar wanda ya sa miliyoyin mutane suka dogara kacokan a kan kayan agaji.

Taron masu bayar da agaji da aka yi a London, ya nemi samar da dala biliyan daya da rabi domin gudanar da ayyukan agaji a cikin shekarar da muke ciki.

Duk wani kokari na kare yunwa a Somaliya na da matukar wuya saboda rikicin da ake fama dashi na masu ikirarin jihadi.

Majalisar Dinkin Duniya da kuma Bankin duniya sun ce a cikin shekarar da muke ciki kadai, ana bukatar dala biliyan daya da rabi yayin da al'ummar kasar Somaliya fiye da miliyan biyar ke bukatar agajin gaggawa.

Nan da wasu watanni masu zuwa akwai yiwuwar za a sake fuskantar matsanancin fari a wasu sassa na kasar, matukar aka gaza hada kudaden da ake bukata domin samar da kayan agaji ga al'ummar kasar ta Somaliya.

Wani jami'in kungiyar agaji ya ce abu ne mai sauki a ciyar da yaro guda da ke fama da matsananciyar yunwa a kan ceto wanda ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.

Labarai masu alaka