''Yan Birtaniya za su yi zanga-zanga' yayin ziyarar Yariman Saudiyya

Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yarima mai shekara 32 ya bankado jami'ai masu cin hanci da rashawa a kasarsa

Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya fara ziyarar kwana uku a Birtaniya a lokacin da ake tsaka da shirya zanga-zangar nuna adawa da rawar da kasarsa ke takawa a yakin Yemen.

Ana ganin Mohammed bin Salman mai shekara 32, a matsayin wanda ke son kawo sauyi a al'adun kasashen Larabawa masu arziki.

Birtaniya na son yin amfani da damar da Saudiyya ta bude a bangaren tattalin arziki, amma kuma za ta nuna damuwarta kan halin ha'ula'i da ake ciki a Yemen.

Ana sa ran mutane za su yi zanga-zangar a wajen fadar Birtaniya da ke Downing Street, don nunawa fushinsu kan kashe fararen hula da ake a Yemen sakamakon hare-haren da rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta ke kai wa - wanda Birtaniya da Amurka ke goyawa - a yaƙin da suke da 'yan tawayen Houthi.

Yariman, wanda ake zaton shi ne magajin gadon Sarki Salman mai shekara 82, yana ziyara ne a karon farko a Birtaniya tun bayan zamowarsa yarima mai jiran gado.

Zai kuma ci abincin dare tare da Mijin Sarauniya Izabel da jikanta Yarima William.

Ana danganta Yariman da mai kawo sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa a kasar da ta ke mai ra'ayin 'yan mazan jiya, kamar janye dokar hana mata tuka mota.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Abubuwa biyar akan Yarima mai jiran gado Mohammed Salman da baku sani ba

Har ila yau, ya kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa a kasar, al'amarin da ya sa aka tsare yarimomi da ministoci da kuma manyan 'yan kasuwa wadanda aka samu kimanin dala biliyan 106 a hannunsu.

Duk da haka, mutane da yawa sun soki matakinsa na shiga fadan Yemen da kuma takunkumin da ya sanyawa Qatar, tare da dakatar da masu adawa da manufofinsa.

Za a kafa sabuwar majalisar hadin gwiwa da za ta iya kawo Saudiyya ta zuba jarin fam biliyan 100 a kasar Birtaniya a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Labarai masu alaka