World Cup: An gabatarwa da Shugaba Buhari kofin duniya a Abuja

buhari Hakkin mallakar hoto Presidency

Hukumar kwallon kafa ta Duniya ta gabatar wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kofin kwallon kafa na duniya wanda za a lashe a gasar cin kofin duniya ta bana a Rasha.

Dazu da rana ne dai kofin ya iso Najeriya - daya daga cikin kasashen da za su fafata a gasar; a ci gaba da rangadin birane 91 da ke kasashe 51 na duniya da kofin ke yi.

Jirgin kamfanin Coca-Cola ne ya kawo 'yan tawagar da ke dauke da kofin inda ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ministan wasanni na kasar Barista Solomon Dalung, ya ce wannan tamkar lasawa Najeriya zuma a baki ne a lashe, "don haka mu ne za mu shanye zumar nan tabbas."

"Wannan abu zai karawa 'yan Najeriya kwarin gwiwar mara wa 'yan wasan kasar baya a lokacin wasan wanda hakan zai iya kai su ga nasara.

"Ya kamata 'yan wasa su yi kokarin ganin yadda shugaban kasarmu ya daga wannan kofi to su yi kokarin ganin sun dawo da kofin Najeriya.

"Ziyarar na da muhimmanci ga irin nasarar da za a samu."

Shugaba Buhari dai ya lashi takobin bayar da cikakken goyon baya ga 'yan wasan kasar don ganin sun samu nasara.

Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Shugaban ya kuma gana da 'yan tawagar kwallon kafar kasar
Hakkin mallakar hoto Presidency

Labarai masu alaka