Dan Nigeria ya zama Sanata a Italiya a karon farko

tony iwobi Hakkin mallakar hoto Tony Iwobi twitter

Wani dan gudun hijira dan Najeriya ya zama dan majalisa bakin fata na farko a kasar Italiya bayan zaben da aka yi a ranar Lahadi - bayan da ya tsaya takara a jam'iyyar da ke adawa da 'yan ci-rani.

Toni Iwobi ya bayyana nasarar da ya samu a shafin sada zumunta na Facebook, yana mai cewa a shirye yake ya fara sabon babi a rayuwarsa.

Mr Iwobi na cikin mambobin kungiyar League ta masu sassaucin ra'ayi, wadda ke goyon bayan saukaka tsauraran matakan korar 'yan gudun hijira da kuma kara toshe wa 'yan ci-rani damarmaki.

Duk da ya kasance shi ma dan ci-rani ne, Mista Iwobi ya kasance mai magana da yawun kungiyar League kan ci-rani tun 2014, ya kuma yi yakin neman zabensa ta hanyar amfani da taken "'Yan ci-rani su daina tuttodowa ba bisa ka'ida ba.

Zaben, wanda jam'iyyarsa ta zo ta uku da kashi 17% na kuri'un da aka kada, wanda hakan gagarumin kari ne 4% a shekara 2013, na zuwa ne a dai dai lokacin da batun 'yan ci rani ke kara zafafa.

Labarai masu alaka