Kamfanin Coca-Cola zai soma yin giya

Coca-Cola bottles Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images

Kamfanin Coca-Cola na shirin soma yin giya karon farko tun da aka kafa shi shekara 125- inda za a rika zuba ta a wata kwalba ta musamman a Japan.

Kamfanin yana so ne ya shiga fafutikar neman riba irin wacce kamfanin Chu-Hi da ke yin lemon kwalba mai gas wanda ake kira shocu.

Lemon kwalbar yana dauke da kashi uku zuwa takwas na barasa.

Wani babban jami'in kamfanin Coke a Japan ya ce an dauki matakin ne "domin samun ribar da ke cikin sayar da irin wadannan lemuka masu barasa a cikinsu".

Da alama ba za a sayar da giyar a ko'ina ba sai a kasar ta Japan.

Shochu na da matukar farin jini musamman a tsakanin mata mashaya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamfanin ya ce Japanawa na matukar sayen lemukansa

Labarai masu alaka

Karin bayani