An nemi gwauraye su daina ruwan ido

china Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kafar yada labaran gwamnati a China tana karfafa gwiwar maza da mata su rage ruwan ido wajen zabar aboki ko abokiyar aure

Kafar yada labaran gwamnati a China tana karfafa gwiwar maza da mata su rage ruwan ido wajen zabar aboki ko abokiyar aure.

Maimakon haka, su hakura da wanda suka samu dan daidai-wa-daida.

Wani sharhi da mashahuriyar jaridar China mai suna People's Daily ta wallafa na cewa gwauraye da yawa kan sak'a wa zuciyarsu cewa sai sun samu zankadediyar mace ko namiji dandasheshe, abin da ke sanya su ture duk wani zabi na babu yabo ba fallasa.

Sharhin jaridar ya zo ne lokacin da ake bayyana damuwa game da raguwar yawan haihuwa a China.

A 'yan shekarun baya ne, hukumomi suka yasar da manufar haifar da daya rak da ta yi kaurin suna, sai dai hakan bai sa an samu karuwar hayayyafar 'ya'yan da ake sa rai ba.

Labarai masu alaka