An kai wa dan leken asirin Russia hari da guba

A na zargin Rasha da yunkurin kashe Mr Skripal Hakkin mallakar hoto EPA/YULIA SKRIPAL/FACEBOOK
Image caption A na zargin Rasha da yunkurin kashe Mr Skripal

Rundunar 'yan sandan Birtaniya masu yaki da ta'addanci ta ce an yi kokarin kashe wani tsohon dan leken asirin Rasha da 'yarsa a birnin Salisbury da wata guba.

Sergei da Yulia Skripal na asibiti cikin matsanancin rashin lafiya tun bayan da a ka tsince su a sume a kan wani benci ranar Lahadi,

Rahotanni sun nuna cewa da alama an sa ma Sergei da Yulia Skripal gubar ne da gangan.

Rundunar 'yan sanda ba ta bayyana ko wace guba ce aka yi amfani da ita wajen kai harin ba.

Sai dai ta ce daya daga cikin 'yan sandan da suka fara zuwa wajen ranar Lahadi na cikin matsanancin yanayi.

Ana dai zargin Rasha da yunkurin kashe Mr Skripal da 'yar sa amma Rashar ta musanta zargin.

Labarai masu alaka