Za a ware Canada da Mexico daga karin harajin karafa

Fadar White House ta ce za a ware kasashen Canada da Mexico daga karin harajin a bisa dalilin tsaron kasa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fadar White House ta ce za a ware kasashen Canada da Mexico daga karin harajin a bisa dalilin tsaron kasa

Gwamnatin Donald Trump ta nuna alamar cewa zata yi sassauci a shirinta na kara haraji kan gorar ruwa da karafa da ake shigowa da su Amurka, yayin da 'yan jam'iyyar Republikan da ke hamayya da sabon shirin su ka matsa wa shugaban lamba.

Fadar White House ta ce za a ware kasashen Canada da Mexico-- wadanda su ka kasance kan gaba wajen samar da karafan ga Amurka --daga karin harajin na wucin gadi a bisa dalilin tsaron kasa.

Firayim Ministan Canada Justin Trudeau ya ce Canada da Amurka na da hadin gwiwa mai karfi ta fuskar tsaron kasa fiye da kowadanne kasashe biyu a duniya. Ya kuma ce su na aiki kut-da kut a kan batun tsaron Amurka kuma mun kasance kawaye a kungiyar tsaro ta NATO.

Sama da 'yan jam'iyyar Republikan dari ne a majalisa su ka sa hannu kan wata wasika inda su ka yi kira ga Shugaba Trump da ya sake duba batun harajin wanda su ka yi gargadin zai iya haifar da mummunan sakamako.

Labarai masu alaka