Birtaniya za ta kashe fam 700,000 don gina gidan kaso a Nigeria

Ana yawan samun cinkoso a gidajen yarin Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yawan samun cinkoso a gidajen yarin Najeriya

Gwamnatin Birtaniya ta fara shirin zuba kudi kusa dala miliyan daya wajen gina sabon bangaren gidan kaso a Najeriya.

Sakataren wajen Birtaniya Boris Johnson wanda ya sanar da haka ya ce akwai yarjejeniyar sauyin gidan kaso na dole tsakanin kasashen biyu.

Yarjejeniyar za ta bai wa wasu fursunoni da su ka cancanta damar a dawo da su domin karasa hukuncinsu a kasashensu.

Sabon ginin bangaren da Burtaniya za ta yi dai zai dauki gadaje 112 ne.

Ana sa ran za a yi aikin ginin ne a gidan yari na Kiri-Kiri da ke jihar Legas.

Wasu alkaluma da Ma'aikatar Shari'a ta Birtaniyar ta fitar sun nuna cewa, akwai fursunonin 'yan Najeriya 320 a gidajen yarin Birtaniya a karshen shekarar 2016, wanda hakan ya dauki kaso uku cikin 100 na yawan fursunonin kasashen waje da ke kasar.

Mista Johnson ya ce hakan zai taimakawa wajen inganta tsarin Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya.

A wata sanarwa da ya aikawa Majalisar Dokokin kasar, ya ce: "Samar da wannan taimako yana cikin tsarin gwamnati na taimakawa Yammacin Afirk ta fannin tsaro."

Takardun kwangila da aka bai wa kamfanin da zai kula da ginin sun nuna cewa za a kashe fam 695,525.

Labarai masu alaka