Zaki ya kai wa wata yarinya hari a Saudiyya

A lion cub. File photo Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption Faisal Ossairy, ya ce wani abun kama gashi da ke makale a kan yarinyar ne ya janyo hankalin zakin har ya sa ya kai mata wafta

An tsare wani mai horar da zaki wanda zakinsa ya kai wa wata yarinya hari a yayin wani biki a Saudiyya, bayan da jama'a sun nuna fushinsu kan faruwar lamarin.

Hukumomi sun ce an kuma tsare wanda ya shirya bikin a Jeddah.

Harin ya afku ne bayan da aka yarinyar da wadansu yara shiga inda aka rufe zakin.

A wani bidiyo da aka fitar, an ga yadda zakin ya rutsa yarinyar, yayin da ya tsuguna a gabanta ya kuma janyp kanta da faratansa. Amma ta samu ta kufce ba tare da jin rauni ba.

Yarinyar, wadda ba a fadi sunanta da shekarunta ba, ta samu ta gudu bayan wani mutum ya rike zakin dan wata shida a kasa.

Shafin intanet na Al-Marsad a Saudiyya ya ruwaito cewa mai koyar da zakin Faisal Ossairy, ya ce wani abun kama gashi da ke makale a kan yarinyar ne ya janyo hankalin zakin har ya sa ya kai mata wafta.

Ya kuma ce an horar da zakin yadda zai yi mu'amala da mutane an kuma cire faratansa.

Bidiyon da aka saka a shafukan sada zumunta ya yadu, wanda hakan ya janyo mutane da yawa suna zargin wadanda suka shirya bikin da rashin kula da lafiyar yaran.

Labarai masu alaka

Karin bayani