Kun taba ganin mutumin da ba ya so a yi masa karin albashi?

Hospital operation Hakkin mallakar hoto stockvisual

Likitocin da ke aiki a yankin Quebec na kasar Canada sun girgiza duniya bayan sun ki amincewa a kara musu albashi.

Me ya sa mutum zai ce ba ya so a yi masa karin albashi?

Su dai wadannan likitoci na Quebec sun ce sun ki amincewa da karin albashi ne saboda a mika kudin wurin kula da lafiyar masu larura.

Wata yarjejeniyar shekara takwas da aka sanya wa hannu a watan Fabrairu za ta bai wa likitoci kusan 20,000 damar samun karin daga kashi 1.4 zuwa kashi 1.8 a kowacce shekara.

Hakan na nufin, yankin na Quebec wanda ke yin tallafi a albashin likitocin, zai ware musu karin $1.2bn zuwa shekarar 2023.

Kungiyar kwadagon da ke wakiltar likitocin, wacce ta sa gwamnati yin karin albashin, ta ce matakin wani adalci ne a gare su.

Sai dai ba dukkan likitocin ne suka ji dadin wannan karin albashi ba - fiye da 700 sun sanya hannu kan wata takarda ta kungiyar likitocin Médecins Québécois Pour le Régime suna masu cewa ba sa bukatar karin albashi.

A cewarsu, ya kamata a yi amfani da kudin wurin yi wa marasa lafiya da sauran masu larura magani.

"Mu likitocin Quebec, muna so a soke karin albashin da aka yi mana sannan a yi amfani da kudin wajen inganta rayuwar ma'aikatan lafiya da marasa lafiyar Quebec," in ji wata sanarwa da suka fitar ranar 26 ga watan Fabrairu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Makonni kadan bayan fitar da wannan sanarwa, an samu karin likita 250 da ke so a soke karin albashin. Akwai kimanin likita 20,000 a yankin na Quebec.

Wannan bukata da suka shigar ta son inganta lafiyar masu larura na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsananta bincike kan harkokin lafiyar kasar.

Ranar Laraba, sakamakon wani bincike da hukumar lafiya da walwalar Quebec mai zaman kanta ta fitar ya nuna cewa an ninka albashin likitocin yankin daga 2005-15, yayin da lokacin da likitocin ke bai wa marasa lafiya ya ragu.

A gefe guda, ma'aikatan jinyar Quebec na fafutikar ganin an inganta yanayin aiki da kuma albashinsu.

Labarai masu alaka