PDP ta sa baki kan batun juyin mulki a Nigeria

PDP Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi kira ga rundunar sojin kasar da kada ta sanya kanta cikin harkokin siyasa.

PDP ta bayyana haka ne bayan rundunar sojin ta yi watsi da wasu kalamai da mataimakin shugaban majalisar dattawa ya yi cewa akwai yiwuwar sojoji su sake kwace mulki a kasar.

Sanata Ike Ikweremadu - dan jam'iyyar PDP - ya fadi hakan ne ranar Laraba a zauren majalisar lokacin da yake nuna damuwarsa ga wasu abubuwa da suka faru da yake ganin bai kamata su faru ba a kasar da ke bin tsarin dimokradiyya ba.

"Wa zai ce sojoji ba za su iya dawowa su karbi mulki ba? abu ne mai yiyuwa ga yadda abubuwa ke tafiya a yanzu." a cewarsa mataimakin shugaban majalisar dattijan.

Ya kara da cewa "matsalar da muke fama da ita a Najeriya ita ce dimokuradiyarmu na ja da baya."

Bai yi laifi ba

Sanarwar da kakakin jam'iyyar ta PDP Kola Ologbondiyan ya aike wa manema labarai ta ce ta kalli "cikakken bidiyon gudunmawar da Sanata Ekweremadu ya bayar a zauren majalisar dattawa kuma ba mu ga wani abu da zai sa hedikwatar rundunar tsaro ta fitar da sanarwa irin wacce ta yi ba."

PDP ta soki kalaman da rundunar sojin ta yi cewa Sanata Ekweremadu yana son zubar da kimarta.

Abubuwan da Sanata Ikweremadu ya fada

Abubuwan da Sanata Ikweremadu ya fada da yake ganin sun sabawa dimokuradiya sun hada da batun rushe gidan Sanata Hunkuyi a Kaduna.

Da kuma yadda aka hanawa tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shiga Kano.

"Muna managa kan kwankwaso wanda aka hana wa zuwa jiharsa da ya mulka tsawon shekaru takwas, mun ga mutane dauke da sanduna suna jiransa a filin jirgi".

"Ina maganar yadda jami'an tsaro suka yi wa Dino Melaye kofar rago, yanzu haka a Kaduna, Shehu Sani bai isa ya shirya wani taro ba".

Kuma a haka wani zai ce wai wannan dimokuradiyar za ta dore, ina ganin ba inda za ta je." a cewar Sanata Ikweremadu.

Rundunar sojin ta kuma fayyace a cikin sanarwar cewa "Rundunar sojin Najeriya yanzu matsayinta ya kai kamar na tsarin kasashen duniya wajen tabbatarwa da kare mulkin demokuradiya.

Hakkin mallakar hoto Twitter

Labarai masu alaka