China ta amince Xi Jinping ya zama shugaban mutu-ka-raba

Xi Jinping walking in front of delegates' tables and empty chairs Hakkin mallakar hoto AFP

Jam'iyya mai mulkin China ta amince a cire wa'adin da ya takaita shekarun da shugaban kasar zai yi yana mulki, abin da ke nufin Shugaba Xi Jinping zai ci gaba da mulki na mutu-ka-raba.

Jam'iyyar National People's Congress ta dauki wannan mataki ne ranar Lahadi a wurin taron da take yi shekara-shekara.

Dama dai an yi tsammanin hakan daga wurin jam'iyyar. Wakilai biyu ne suka ki amincewa da matakin, uku kuma suka kauracewa kada kudi'a, a cikin wakilai 2,964 da suka kada kuri'arsu.

A shekarun 1990 ne China ta sanya wa'adin mulki sau biyu a kundin tsarin mulkinta.

An yi hakan ne domin hana shugaban kasar ya zama tamkar Mao Zedong, inda za a samu wanda zai rika shugabanci tare da tafiya da mutane ba wanda zai zama shugaban kai-kadai-gayya ba.

Wakilin BBC a Beijing, Stephen McDonell, ya ce yanzu shugaban na China ya samu karfin ikon da aka dade ba a ga irinsa a tarihin kasar ba.

Mr Xi ya kauce wa al'adar gabatar da mutumin da zai gaje shi lokacin babban taron jam'iyyar Communist Party a watan Oktoban da ya wuce.

Labarai masu alaka