Jam'iyyar APC ce kan gaba a zaben shugaban kasar Saliyo

Mutum miliyan uku ne ake sa ran sun kada kuri'unsu a Saliyo a zaben bana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutum miliyan uku ne ake sa ran sun kada kuri'unsu a Saliyo a zaben bana

Hukumar zaben Saliyo ta sanar da kwarya-kwaryar sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Laraba.

Kashi 50 cikin dari na sakamakon zaben da aka fitar ya nuna cewa jami`yyar APC mai mulki ce a kan gaba.

Shugaban hukumar Mr Mohammed Nfah Conteh ya ba al`uma hakuri saboda jinkirin da hukumarsa ta yi kafin ta sanar da bangaren sakamakon.

Ya ce "Mr Kamara Samura na All Peoples Congress ya samu kuria 566, 113, haka kuma Mr Bio Julius Maada ya samu kuri`a 564, 687.

"Wannan shi ne sakamakon kashi 50 cikin dari na kuri`un da aka kidaya, wadanda kuma hukumar zabe ta tantance su. Wannan kwarya-kwaryar sakamako ne, don haka ba shi ne cikakken sakamakon zaben ba."

A nan gaba kadan ne ake sa ran hukumar za ta sanar da cikakken sakamakon zaben, wanda mutum goma sha shida ke takarar shugabancin kasar.

Mata biyu da ke takarar shugabancin kasar, su ma da wuya su yi wani tasiri kasancewar daya ta samu kuri`a dubu 6 da `yan kai, yayin da daya kuma ta samu dubu daya da dari shida.

Ya zuwa yanzu dai babu wani bangaren magoya baya da ya fara murna saboda jin kwarya-kwaryar sakamakon zaben.

A Saliyo dai ba kasafai ake zaben shugaban kasa ba tare da shiga zagaye na biyu ba.

Kuma ganin cewa tazarar da ke tsakanin dan takakar jam`iyya mai mulki da na babbar jam`iyyar hamayya kadan ce, wasu masana sun fara hasashen cewa watakila a yi zabe zagaye na biyu.

Labarai masu alaka