Tsawa ta kashe mutum 16 a Rwanda

map showing Rwanda and Burundi with the former's capital Kigali marked out.

Watsa ta kashe akalla mutum 16 sannan ta jikkata da dama a wata Coci mai suna Seventh-Day Adventist da ke Rwanda ranar Asabar.

Yawancin mutanen da lamarin ya shafa sun mutu ne nan take bayan tsawar ta fada kan Cocin da ke lardin Nyaruguru na kudancin kasar, in ji wani magajin lardin Habitegeko Francois a hirarsa da kamfanin dillancin labaran AFP.

Biyu daga cikin mutanen sun mutu ne sakamakon raunin da suka samu, sannan an garzaya da mutum 140 asibiti.

Magajin lardin ya kara da cewa tsawar ta kashe wani dalibi ranar Jumma'a.

Tsawar, wacce ta faru a lardin mai cike da duwatsu da ke kan iyaka da Burundi da tsakar ranar Asabar a garin Gihemvu, ta auka wa mutane ne suna tsaka da addu'o'i a Cocin.

"Likitoci sun ce mutum uku ne kawai ke cikin mawuyacin hali amma suna samun sauki," in ji Mr Francois.

Ya kara da cewa tsawar da ta faru ranar Jumma'a ta fada kan mutum 18 amma mutum daya ne ya mutu.

Rahotanni sun ce har yanzu dalibai uku na karbar magani a asibit yayin da aka sallami sauran.

Labarai masu alaka